Za a ɗauki ma’aikatan lafiya 20,000, kaso 60% nas da ugozoma, za a kuma inganta aikin

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da sabon tsarin bunƙasa aikin nas da ungozoma domin ƙara yawan ma’aikatan lafiya da tabbatar da samun Universal Health Coverage (UHC) da cimma manufofin ci gaba mai ɗorewa (SDGs).

Times Hausa ta tattaro cewa, Ministan Lafiya, Muhammad Pate, ya bayyana hakan ne a babban taron Nursing Summit da aka gudanar a Abuja, inda aka ƙaddamar da Nigerian Strategic Directions for Nursing and Midwifery (NSDNM) 2025–2030.

Pate ya bayyana nas da ungozoma a matsayin ginshiƙai wajen kula da lafiya a ƙasar nan, yana mai cewa sabon shirin zai taimaka wajen inganta ilimi, ci gaban aiki, da jawo ƙwararru su zauna a cikin ƙasa.

Ya ce shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da ɗaukar sabbin ma’aikatan lafiya kusan 20,000, inda kaso 60 cikin ɗari daga cikinsu za su kasance nas da ungozoma.

“Ba wai horo kaɗai ake buƙata ba – dole ne mu samar da kayan aiki da muhalli mai kyau,” in ji shi.

Shugaban Hukumar Kula da Nas da Ungozoma, Ndagi Alhassan, ya bayyana cewa duk da an ƙara yawan nas daga 23,000 zuwa 115,000, akwai giɓin aikin.

Ya ce ana aiwatar da shirin Community Nursing and Midwifery domin al’ummomi su ɗauki nauyin masu karatu sannan su yi musu aiki bayan sun kammala karatun.

A nasa jawabin, wakiliyar WHO, Mary Brantuo, ta gargaɗi cewa duniya za ta fuskanci giɓi na kusan nas da ungozoma miliyan 4.8 nan da 2030, inda Afirka da Asiya za su fi shan fama.

Haka kuma, wakilin UNFPA a Najeriya, Koessan Kuawu, ya bayyana cewa hukumar ta na tallafa wa shirin horar da ungozoma, inda ya ce “kowacce dala 1 da aka saka a aikin ungozoma na dawo da ribar dala 16.”

Sanata Ipalibo Banigo, shugabar kwamitin lafiya ta Majalisar Dattawa, ta tabbatar da cewa majalisa za ta ci gaba da tallafa wa dokoki da manufofi da za su ƙarfafa aikin nas da ungozoma a faɗin Najeriya.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Leave A Reply

Your email address will not be published.