Yanzu duk wata kwangila da ba ta haura naira biliyan 20 ba kamfani ɗan Najeriya ne zai na yi – Minista
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗaukar sabon tsarin fifita ayyuka wajen biyan kuɗaɗen ayyukan gine-ginen hanyoyi da kamfanin NNPCL ya bari a hannunta, domin tabbatar da ci gaba da aiwatar da su cikin inganci da daidaito da umarnin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Wakilinmu ya tattara cewa, Ministan Ayyuka, Sanata Injiniya David Umahi, ya bayyana hakan ne yayin duba aikin faɗaɗa hanyar Eleme Junction zuwa Onne Port Junction a jihar Rivers, wanda kamfanin Reynolds Construction Company (RCC) ke gudanarwa, a ranar 9 ga Satumba, 2025.
Umahi ya ce ma’aikatarsa ta tattara dukkan ayyukan hanyoyi da NNPCL ta bari, kuma ta gabatar da su ga Shugaban Ƙasa domin tabbatar da cewa ba a dakatar da su ba.
“Shugaban ƙasa ya bayar da umarnin cewa duk wani aiki a ƙarƙashin tsarin harajin NNPC ba zai tsaya ba. Amma muna ba da fifiko kan muhimman hanyoyi da ke cikin muhimman sassan tattalin arziƙin ƙasa,” in ji shi.
Ministan ya yi gargaɗin cewa ma’aikatarsa za ta shigar da hukumomin yaƙi da cin hanci idan aka gano keta ƙa’idoji a cikin kwangilolin ayyukan hanyoyi.
Ya kuma nuna damuwa da yadda wasu ƴan kwangila ke barin hanyoyi ba su kammala matakan shimfiɗa kwalta ba, wanda hakan ke haddasa lalacewar hanyoyi cikin sauri.
Haka kuma, Umahi ya bayyana cewa daga yanzu duk wata kwangila da ta ke ƙasa da naira biliyan 20 za a bai wa kamfanonin cikin gida ne kawai, domin aiwatar da manufar “Nigeria First” da gwamnati ta ɗauka.
Ya yabawa RCC bisa ingancin aikin da take yi, amma ya bayyana rashin gamsuwarsa da yanayin aiwatar da shi, yana mai cewa ranar 15 ga Disamba, 2025 ce ta ƙarshe don kammalawa ba tare da ƙarin lokaci ba.
A yayin da yake duba sauran ayyukan, Umahi ya gargaɗi direbobi masu ajiye manyan motoci a kan hanyoyin Najeriya da su daina, yana mai cewa gwamnati za ta ɗauki mataki tare da ƴan sanda da gwamnoni wajen hana hakan.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook