Wani saurayi ya yi ajalin tsohuwar budurwarsa shekaru biyu bayan rabuwarsu

47

Times Hausa ta sami rahoton cewa, wata matashiya, Deborah Moses, wadda aka fi sani da Deb’rah Porsche, ta rasa ranta a Lagos bayan da tsohon saurayinta, Lintex Ogale, ya kai mata hari, kusan shekaru biyu bayan ta kawo ƙarshen dangantakarsu.

Lamarin ya faru ne da yammacin Alhamis a cikin unguwar da take zaune a Lagos.

An tabbatar da cewa wanda ake zargi ya shiga hannun ƴan sanda kuma ana tsare da shi a halin yanzu.

Wani na kusa da iyalan marigayiyar, Meddy Olutu Imanoel ne ya bayyana al’amarin a cikin wani saƙon Facebook a jiya Juma’a bayan tattaunawa da ƙanwar Deborah.

Ya bayyana cewa Deborah ta kawo ƙarshen dangantakar da ke tsakaninsu da tsohon saurayin nata a watan Agusta 2023 saboda cin zarafi da take zargin yana yi mata.

Sai dai wanda ake zargin ya ƙi yarda ya rabu da ita, yana mai yawan yi mata barazana da cewa “Idan ban aure ki ba, jini zai zuba.”

A cewar ƙanwarta, marigayiya Deborah – wadda kwanan nan ta kammala NYSC kuma ta fara aiki – ta guje wa tsohon saurayinta iya bakin iyawarta.

A daren Alhamis, wanda ake zargin ya sa kayan masu rabon kayan da aka siya domin ya samu damar shiga cikin unguwar.

Bayan ta ƙi fitowa ta karɓi abin da aka ce an kawo mata, sai ya tsallaka katanga ya haura gidan.

“Da farko ya fasa mata tukunyar gas ɗinta da nufin ƙona gidan, da hakan ya ci tura, sai ya kutsa cikin gidan da wuƙa, ya sossoka mata sau da dama,” in ji Imanoel a cikin bidiyo da ya yaɗu a yanar gizo.

Shaidu sun bayyana cewa maƙwabta sun yi gaggawar zuwa wurin bayan jin ƙarar kukanta.

Yayinda wanda ake zargin ya kwanta kusa da ita yana basajar ya mutu, amma daga bisani aka gano yana raye kuma aka kama shi.

Wani daga yankin da abin ya faru mai suna Adoga Israel, ya tabbatar da faruwar lamarin a shafin intanet, yana kira ga al’ummar Igede da su tashi tsaye wajen neman adalci.

Ƙoƙarin PREMIUM TIMES na jin ta bakin ƙanwarta bai yi nasara ba, haka kuma kira da saƙonnin da aka aike wa rundunar ƴan sanda ta Lagos basu sami amsa ba zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

2 Comments
  1. Adamu says

    Gsky Bai kyauta ba wannan Saurayin abun da yayi haka ya nunawa wasu hanya

  2. Adamu says

    Gsky Bai kyauta ba wannan Saurayin abun da yayi haka ya nunawa wasu hanya

Leave A Reply

Your email address will not be published.