Wani darakta a Hukumar Kula da Kogin Sokoto Rima ya faɗa komar ICPC, kotu ta yanke masa hukuncin shekaru shida
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa a Ma’aikatun Gwamnati (ICPC) ta samu nasarar gurfanar da Daraktan Harkokin Gudanarwa na Hukumar Bunƙasa Kogin Rima Sokoto (SRRBDA), Rabiu Musa Matazu, inda kotu ta same shi da laifin karkatar da kuɗaɗen gwamnati zuwa aljihunsa.
Rahoton da wakilinmu ya tattara daga sanarwar ICPC ya bayyana cewa, Matazu ya gurfana a gaban Mai Shari’a Abbas Bawule na Babbar Kotun Jihar Katsina, ƙarƙashin shari’a mai lamba KTH/7C/2022, kan tuhume-tuhume guda huɗu da suka shafi cin amanar aiki da kuma amfani da ofis ba bisa doka ba.
Masu gabatar da ƙara daga ICPC sun bayyana cewa wanda ake tuhumar ya karɓi kuɗi naira dubu dari uku da biyar (₦305,000) daga abokinsa Lawal Dan Sarki, kuɗaɗen haya daga filayen hukumar, amma ya karkatar da su domin amfanin kansa.
Kotun ta samu Matazu da laifin bayan shari’ar da ta ɗau tsawon shekaru uku, inda aka yanke masa hukuncin watanni shida a kurkuku ko kuma tarar naira dubu ashirin a kan tuhumomin farko, na biyu da na uku, sannan aka yanke masa hukuncin shekara biyar a kurkuku ba tare da zaɓin tara ba a kan tuhuma ta huɗu, inda hukuncin zai gudana a lokaci guda.
Wani daga cikin tuhume-tuhumen ya nuna cewa Matazu ya yi amfani da matsayinsa wajen amfana da kuɗin haya na hukumar wanda ya karkatar domin kansa, abin da ya saɓawa sashe na 19 na dokar ICPC ta 2000.
Wannan hukunci, a cewar hukumar, na nuni da jajircewar ICPC wajen tabbatar da cewa ba za a yi amfani da ofishin gwamnati domin amfanin kai ba, tare da tabbatar da cewa duk wanda ya karya doka zai fuskanci hukunci.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook