Tinubu ya buƙaci gwamnonin APC su goyi bayan samar da ƴan sandan jihohi da ƴancin ƙananan hukumomi

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da sauran shugabannin jihohi da su mara wa shirin kafa ƴan sandan jihohi da kuma aiwatar da cikakken ƴancin ƙananan hukumomi, domin ƙarfafa tsaro da inganta shugabanci a Najeriya.

Shugaban ya yi wannan kiran ne a zama na 14 na Kwamitin Ƙoli na APC (National Caucus) da aka gudanar a Abuja, inda ya jaddada cewa ƙalubalen tsaro da ke ƙara ƙamari a Najeriya na buƙatar sabbin hanyoyi masu ƙarfi da dacewa da yanayin kowace jiha.

Tinubu ya kuma buƙaci gwamnonin su mutunta hukuncin Kotun Ƙoli kan ƴancin ƙananan hukumomi, yana mai cewa ba wai kawai kotu ta yanke hukunci ba ne, dole ne kuma kuɗaɗen rabon ƙananan hukumomi su riƙa zuwa musu kai tsaye ba tare da wani katsalandan ba.

“Ba zai wadatar kotu ta yanke hukunci kawai ba. Dole ne kuɗaɗen da aka ware wa ƙananan hukumomi su riƙa isa gare su kai tsaye domin su iya aiwatar da ayyukan raya ƙasa,” in ji Tinubu.

Shugaban ƙasar ya kuma buƙaci jam’iyyar APC da ta ƙara shigar da mata cikin Kwamitin Ƙoli, domin tabbatar da daidaito tsakanin jinsi da kuma ƙarfafa rawar mata a harkokin siyasa.

Kiran kafa ƴan sandan jiha na ƙara ƙarfi ne a daidai lokacin da ake fuskantar matsalolin tsaro da suka haɗa da garkuwa da mutane, hare-haren ƴan bindiga da rikice-rikicen cikin gida a sassa daban-daban na ƙasar nan.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Leave A Reply

Your email address will not be published.