Tinubu ya ba da umarnin gaggawa ga ministoci na rage tsadar kayan abinci a Najeriya

11

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya bai wa wani kwamiti na Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) umarnin gaggawa kan rage tsadar kayan abinci a kasuwannin ƙasar.

Wakilinmu ya tattaro daga jawabin Ƙaramin Ministan Harkokin Noma da Tsaron Abinci, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja.

Sanata Abdullahi ya ce, “Shugaban ƙasa ya bayar da umarni kai tsaye ga kwamiti na FEC da ke duba hanyoyin da za mu tabbatar da cewa kayan abinci da amfanin gona suna samun kariya yayin jigilarsu a kan hanyoyi daban-daban a ƙasa.”

Ya ƙara da cewa manufar shugaba Tinubu ta “food sovereignty” tana nufin tabbatar da wadatar abinci, samun sauƙin siya, da kuma dacewar inganci da sinadaran abinci mai gina jiki a kan tushe mai ɗorewa.

Ministan ya yi bayani cewa, tsadar jigilar amfanin gona na daga cikin dalilan samun hauhawar farashin kayayyaki.

“Idan ka ga irin kuɗin da ake kashewa wajen jigilar kayayyaki kafin su isa kasuwa, za ka gane dalilin da yasa suke tsada sosai,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa gwamnati na aiki tuƙuru wajen ganin an magance matsalolin da ke hana rage tsadar abinci, tare da tabbatar da cewa ƴan ƙasa sun more sauƙin farashin kayayyaki a kasuwanni.

Leave A Reply

Your email address will not be published.