Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da sauya sunan Federal University of Medical Sciences, Azare, da ke Jihar Bauchi, zuwa Jami’ar Sheikh Dahiru Usman Bauchi, domin girmamawa da ɗaukaka sunan fitaccen malamin addinin Musulunci marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Shugaban Ƙasar ya bayyana wannan matsaya ne a ranar Asabar yayin da yake ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayin a gidansa da ke Bauchi.
Tinubu ya ce matakin sauya sunan jami’ar an yi shi ne domin tabbatar da cewa tarihin Sheikh Dahiru Bauchi da gudummawar da ya bayar ga bil’adama da ilimin addini ba za su taɓa gushewa ba.
“Daga yau, ina sanar da wannan sauyin suna domin raya tarihinsa. Federal University of Medical Sciences, Azare, Jihar Bauchi, daga yau za a san ta da suna Jami’ar Sheikh Dahiru Usman Bauchi. Allah Ya albarkaci tarihinsa,” in ji Shugaba Tinubu a jawabinsa.
Shugaban Ƙasar ya bayyana rasuwar malamin a matsayin “babban rashi na ƙasa baki ɗaya,” yana mai cewa rayuwar Sheikh Dahiru Bauchi ta kasance cike da tawali’u, sadaukarwa ga al’umma, da jajircewa wajen yaɗa Musulunci, zaman lafiya da haɗin kai.
Ya kuma roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da Ya jiƙan marigayin da rahama tare da saka shi cikin Aljannar Firdausi.
Hakazalika, Tinubu ya yi addu’ar Allah Ya ba iyalan marigayin ƙarfi da haƙuri, tare da gwamnatin Jihar Bauchi da al’ummarta, domin jure wannan babban rashi.
Ya kuma yi kira ga ƴan Najeriya da su ci gaba da yin addu’o’i domin zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.
Da yake mayar da jawabi a madadin iyalan marigayin, babban ɗansa, Sheikh Ibrahim Dahir Usman Bauchi, ya miƙa godiya ga Shugaban Ƙasa bisa ziyarar ta’aziyya, addu’o’i da kuma girmamawar da aka yi wa mahaifinsu.
Ya kuma yabawa Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, bisa irin goyon bayan da yake bai wa iyalan tun bayan rasuwar malamin.
A nasa jawabin, Gwamna Bala Mohammed ya gode wa Shugaban Ƙasa bisa wannan gagarumar karramawa da ya yi wa iyalan marigayin da Jihar Bauchi gaba ɗaya.
Ya bayyana matakin a matsayin amincewa da irin gagarumar gudummawar da Sheikh Dahiru Bauchi ya bayar, wadda za ta ci gaba da rayuwa har abada.
TIMES HAUSA ta fahimci cewa Shugaba Tinubu ya samu rakiyar manyan jami’an gwamnati da suka haɗa da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas; Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni; da Seyi Tinubu, tare da wasu manyan jami’ai.
Rahotanni sun nuna cewa Shugaban Ƙasar ya sauka a Filin Jirgin Sama na Sir Abubakar Tafawa Balewa International Airport, Bauchi, da misalin ƙarfe 4:09 na yamma, inda Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta tarɓe shi da girmamawar faretin girmamawa.
Daga cikin waɗanda suka tarbe shi a filin jirgin saman akwai Gwamna Bala Mohammed, Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang; Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, Farfesa Ali Pate; Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar; da Sanatan Bauchi ta Kudu, Shehu Buba.
Ziyarar ta’aziyyar na daga cikin jerin ayyukan Shugaban Ƙasa na jajanta wa iyalai da mabiyan marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda tasirinsa da gudummawarsa ga ilimin addinin Musulunci suka ɗauki tsawon shekaru masu yawa a faɗin Najeriya da ma ƙasashen waje.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook