Sowore ya ƙi janye kalaman da DSS ta ce na “ƙarya, ɓatanci, kuma abin tayar da hankalin jama’a” ne kan Tinubu

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Ƙwararren ɗan fafutuka kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar AAC a zaɓen 2023, Omoyele Sowore, ya ƙi amincewa da buƙatar hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) wacce ta nemi ya janye wani rubutu da ya wallafa a dandalin sada zumunta na X, wanda ya shafi Shugaba Bola Tinubu.

Wakilinmu ya tattaro daga wata takardar koke da DSS ta aike masa a ranar 7 ga Satumba, wacce Uwem Davies ya sanya hannu a madadin Daraktan Hukumar, inda aka bayyana rubutun da Sowore ya yi ranar 26 ga Agusta a matsayin “ƙarya, ɓatanci, kuma abin tayar da hankalin jama’a.”

Hukumar ta umarci Sowore da ya janye maganarsa nan take, ya wallafa neman yafiya a jaridun ƙasa guda biyu da tashoshin talabijin guda biyu, tare da miƙa kansa a ofishin hukumar da ke Abuja cikin mako guda.

Sai dai a martanin da ya fitar ranar Juma’a a X, Sowore ya bayyana buƙatar hukumar a matsayin wadda “ba ta da tushe, kuma ba bisa doka ba.”

Ya ce, “Doka ta bayyana cewa mutum kaɗai wanda aka zarga shi ne zai iya shigar da ƙara. Don haka, DSS ba ta da hurumin neman in janye magana a madadin Shugaban Ƙasa.”

Ya zargi hukumar da zama kayan aiki ga gwamnatoci masu mulkin kama-karya, tare da tunawa da yadda aka tsare shi sau da dama a baya bisa laifukan da ya bayyana a matsayin ƙirƙira.

“Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam sun daɗe suna tabbatar da cewa dokokin ɓatanci na laifin ɗabi’a an soke su tun shekarar 1985,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa ƴancin faɗar albarkacin baki ginshiƙi ne a dimokuraɗiyya.

“Ba DSS ke da ikon faɗa min yadda zan yi suka ba. Ƙudurin ƴan Najeriya na ƙwato ƙasarsu daga hannun ɓarayi ba zai taɓa gushewa ba,” in ji Sowore.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Leave A Reply

Your email address will not be published.