Saudiyya ta yi nasarar raba tagwayen da aka haifa a manne a Kano bayan tiyata mai haɗarin gaske

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Wasu tagwaye, Hassana da Husaina, ƴan asalin Jihar Kano, sun dawo Najeriya bayan samun nasarar tiyata mai matuƙar wahala da aka yi musu a ƙasar Saudiyya, inda aka raba jikinsu da ya haɗu a ƙasan ciki, ƙugu da ƙashin baya.

Tagwayen sun sauƙa a Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano tare da jami’an Saudiyya suka tarbe su cikin farin ciki.

“Wannan ba nasarar aikin kiwon lafiya kaɗai ba ba ne, nasarar ɗan Adam ce (gaba ɗaya),” inji Gwamna Yusuf.

Ya ƙara da cewa Kano za ta ɗauki nauyin kula da ilimi da ci gaban rayuwar yaran baki ɗaya.

Tiyatar wadda aka gudanar a Asibitin Yara na King Abdullah a Riyadh, ta gudana bisa umarnin Sarkin Saudiyya Salman bin Abdulaziz Al-Saud da Yarima Mohammed bin Salman.

Likitoci 38 daga fannoni daban-daban ne suka jagoranci aikin, wanda ya ɗauki awanni 14 a matakai tara daban-daban.

Babban likitan tiyatar, Dr Abdullah Al-Rabeeah, ya bayyana aikin a matsayin ɗaya daga cikin mafi wahala da suka taɓa gudanarwa a tarihi.

“Nasara irin wannan na ba wa iyalai da dama a duniya ƙwarin gwiwa,” inji shi.

Shirin raba ƴan tagwaye a Saudiyya ya gudanar da rabe-rabe 65 cikin shekaru 35, inda aka taimaka wa fiye da tagwaye 150 daga ƙasashe 25.

Jakadan Saudiyya a Kano, Khalil Ahmed Al-Admawi, ya bayyana cewa nasarar ta nuna yadda Saudiyya ke fifita taimakon rayuwar ɗan Adam.

Tagwayen yanzu suna ci gaba da samun kulawar lafiya a asibiti a Kano, tare da alƙawarin gwamnatin jihar na tallafawa rayuwarsu gaba ɗaya.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Leave A Reply

Your email address will not be published.