Sakamakon zaman Majalisar Zartarwa ta Jigawa na ranar Talata 16 ga Satumba
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Umar Namadi, ta gudanar da zamanta na yau da kullum a ranar Talata, 16 ga Satumba, 2025, inda aka amince da wasu manyan matakai da za su shafi muhimman fannoni na rayuwar al’umma.
Wakilinmu ya tattaro cewa shawarwarin da aka cimma sun haɗa da ɓangaren muhalli, tattalin arziƙi, ilimi, lafiya da kasafin kuɗi.
Ƙirƙirar kwamiti kan muhalli da amfani da sabbin na’urori
Daga cikin manyan shawarwarin, majalisar ta amince da kafa kwamiti na musamman don samar da tsarin amfani da na’urorin girki na zamani (clean cookstoves) da na’urar busar da shinkafa ta hasken rana a faɗin jihar.
Wannan mataki ya biyo bayan gabatarwar kamfanin Dare Carbon Limited a gaban majalisar, inda aka nuna muhimmancin tsarin wajen rage sare dazuka, inganta tsaron abinci da kuma ƙirƙirar ayyukan yi a ɓangaren muhalli.
Kwamitin zai ƙunshi Kwamishinan Muhalli a matsayin shugaba, Kwamishinan Noma, Kwamishinan Lantarki da Makamashi, Babban Daraktan Hukumar Ƙarfafa Tattalin Arziƙi, da kuma Babban Sakataren Harkokin Sabbin Hanyoyin Makamashi a matsayin sakataren kwamiti.
Bincike kan rashin biyan 1% na ayyukan gwamnati
Hakazalika, majalisar ta amince da rahoton kwamitin da ya binciki batun rashin bin doka wajen cire 1% daga kuɗin kwangila na ma’aikatu daban-daban.
Rahoton ya gano gazawa da dama wajen bin ƙa’idar, inda ya ba da shawarwari na ladabtarwa da gyara.
An umarci dukkan ma’aikatu da su bi umarnin, yayin da Ma’aikatar Kuɗi za ta sa ido wajen tabbatar da bin dokar.
Gina sabbin ajujuwa a makarantu
Majalisar ta kuma amince da kashe naira miliyan 228.9 domin gina sabbin ajujuwa uku-uku a makarantu takwas na Government Day Arabic Senior Secondary Schools (GDASSS) a faɗin jihar.
Wannan aikin zai rage cunkoson ɗalibai da inganta yanayin koyo da koyarwa.
Kafa ƙa’idoji na kulawa da lafiyar uwa da ɗa
Wakilinmu ya gano cewa majalisar ta amince da ƙa’idojin aiki don aiwatar da shirin kula da lafiya kyauta ga mata masu juna biyu, jarirai da ƙananan yara a cibiyoyin lafiya na mataki na farko da na biyu.
Wannan mataki zai tabbatar da tsari, daidaito da inganci wajen kula da marasa lafiya a faɗin jihar.
Ƙarin kasafin kuɗin shekarar 2025
A ƙarshe, majalisar ta amince da ƙarin kasafin kuɗin shekarar 2025 domin magance sabbin buƙatu da kuma ƙarfafa ayyuka a sassa masu muhimmanci.
Kuɗin ya haɗa da naira biliyan 58 ga gwamnatin jiha da naira biliyan 17 ga ƙananan hukumomi 27.
Za a tura wannan kasafin majalisar dokokin jiha domin amincewa.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook