PDP ta dakatar da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar masu goyon bayan Nyesom Wike

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta dakatar da wasu manyan jiga-jiganta guda huɗu – Lauyan Jam’iyya, Kamaldeen Ajibade (SAN); Sakataren Ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu; Mataimakin Lauyan Jam’iyya, Okechukwu Osuoha; da Sakataren Shirye-shirye na Ƙasa, Umaru Bature – na tsawon wata ɗaya, bayan hukuncin kotu da ya dakatar da shirin gudanar da taron gangamin ƙasa na jam’iyyar.

TIMES HAUSA ta tattaro cewa, Mai magana da yawun jam’iyyar, Mista Debo Ologunagba, ne ya bayyana hakan bayan wata  ganawar gaggawa da Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC) a hedkwatar jam’iyyar da ke Maitama, Abuja.

Ologunagba ya bayyana cewa, bisa ga Sashe na 36(2) na Kundin Tsarin PDP, Mataimakin Sakataren Ƙasa, Hon. Setonji Koshoedo, zai riƙe muƙamin a matsayin mai riƙon ƙwarya, yayin da Daraktan Harkokin Shari’a, Jacob Otorkpa, zai kula da sashen shari’a na jam’iyyar.

Ya ce, “An ɗauki wannan mataki ne bayan nazarin ayyukan wasu mambobi da suka saɓa da tsarin jam’iyya. Waɗannan mambobi sun aikata abubuwan da suka saɓawa Sashe na 58 na kundin tsarinmu, ciki har da yin abinda zai ɓata sunan jam’iyya, rashin biyayya ga umarnin jam’iyya, da haifar da rashin jituwa tsakanin mambobi.”

An kuma dakatar da Ajibade da Osuoha na tsawon kwanaki 30, sannan kuma an miƙa lamarinsu ga kwamitin ladabtarwa.

Haka kuma, Sakataren Shirye-shirye, Hon. Umaru Bature, da Sakatare na Ƙasa, Sanata Anyanwu, sun shiga cikin jerin waɗanda aka dakatar, tare da tura batun nasu zuwa kwamitin ladabtarwa.

Wannan rikici ya samo asali ne daga shirin gudanar da babban taron jam’iyyar da aka tsara a Ibadan, Jihar Oyo, a ranar 15–16 ga Nuwamba, wanda yanzu aka dakatar bayan wata kotu ta bayar da umarni a ranar Juma’a cewa jam’iyyar ta dakatar da taron har sai ta daidaita al’amura da dokokinta.

Alƙalin da ya jagoranci shari’ar, Mai Shari’a James Omotosho, ya bayyana cewa PDP ta karya dokar kundinta, dokar ƙasa ta 1999 da kuma Dokar Zaɓe ta 2022 saboda rashin gudanar da sahihan tarukan jihohi kafin sanar da taron ƙasa.

Masu shigar da ƙarar sun haɗa da shugabannin jam’iyyar a jihohin Imo, Abia da yankin Kudu maso Kudu, waɗanda suka zargi PDP da saɓa wa dokokinta na cikin gida.

Wannan mataki ya ƙara girgiza jam’iyyar, wadda ke fama da rikice-rikicen cikin gida musamman tsakanin magoya bayan Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da muƙaddashin shugaban jam’iyyar, Ambasada Umar Damagum.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Leave A Reply

Your email address will not be published.