NNPP ta bayyana cewa babu ruwanta da shirin Kwankwaso na komawa APC

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Sakataren New Nigeria Peoples Party (NNPP) na ƙasa, Dr Ogini Olaposi, ya bayyana cewa shirin shiga All Progressives Congress (APC) na tsohon gwamnan Kano, Senator Rabiu Kwankwaso da Kwankwasiya Movement ne kaɗai, ba jam’iyya ba.

Wakilinmu ya tattaro cewa Olaposi ya faɗi hakan ne a ranar Litinin a Legas, yana mai cewa Kwankwaso da mabiyansa sun yanke cewa suna son shiga APC, amma wannan ba ya shafar jam’iyyar NNPP.

Olaposi ya ce, “Kwankwaso ba ya da jam’iyyar siyasa a yanzu. Duk wata tattaunawa da ake yi da shi a madadin NNPP ba ta da tasiri.”

Ya kuma bayyana cewa yarjejjeniya tsakanin NNPP da Kwankwasiya Movement ta ƙare bayan zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Ya yi kira ga ƴan Najeriya da su fahimci cewa duk wata tattaunawa da Kwankwaso ya yi yana a matsayin ɗan ƙasa ne kawai, ba memba na NNPP ba.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Leave A Reply

Your email address will not be published.