NiMet ta yi hasashen samun ruwan sama da guguwar iska a yau Litinin a sassan Najeriya

27

Wakiliyarmu Maryam Ayuba ta tattaro daga Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMet) cewa hasashen yanayi na ranar Litinin, 8 ga Satumba, 2025, daga ƙarfe 12 na dare zuwa ƙarfe 11:59 daren Talata, ya nuna ana sa ran samun ruwan sama da guguwar iska a sassa da dama na ƙasar.

A yankin Arewa, an bayyana cewa safiyar Litinin za ta kasance da gajimare tare da hasken rana jifa-jifa, sannan a samu ruwan sama mai ɗaukewa lokaci-lokaci da guguwa a sassan Taraba da Adamawa.

Da rana zuwa yamma kuma, ana sa ran samun guguwar iska da ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a jihohin Borno, Sokoto, Kebbi, Yobe, Gombe, Bauchi, Kaduna, Adamawa, Jigawa, Kano, Katsina, Zamfara da Taraba.

A yankin Tsakiyar Ƙasa kuma, ana sa ran samun ruwan sama marar ƙarfi a safiyar Litinin a FCT, Nasarawa, Benue, Niger da Kogi, yayin da yammacin rana zuwa dare za a iya samun guguwar iska a Nasarawa, Niger, Plateau, Kogi, Kwara, Benue da FCT.

A Kudancin Ƙasar kuma, safiya za ta kasance da gajimare tare da yiyuwar samun ruwan sama marar yawa a Enugu, Ebonyi, Imo, Abia, Cross River da Akwa Ibom, sannan daga rana zuwa dare ana iya samun ruwan sama jifa-jifa a Oyo, Ondo, Osun, Ekiti, Lagos, Edo, Delta, Enugu, Ebonyi, Abia, Imo, Anambra, Bayelsa, Rivers, Cross River da Akwa Ibom.

NiMet ta ja hankalin jama’a da su yi taka-tsantsan a lokutan guguwar iska, inda za a iya samun iska mai ƙarfi wadda ka iya rage hangen nesa, sanya tituna su zama masu matsala da kawo tsaiko ga harkokin waje.

Ta kuma yi gargaɗi ga al’ummomin da ke yankunan da ambaliyar ruwa ke samuwa su kasance cikin shiri.

Leave A Reply

Your email address will not be published.