Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Hukumar Hasashen Yanayi ta Ƙasa (NiMet) ta yi hasashen cewa za a samu guguwar iska da ruwan sama mai matsakaicin yawa a sassan Najeriya daga Litinin 14 ga Satumba zuwa Laraba 16 ga Satumba.
Wakiliyarmu ta tattaro daga sanarwar da aka fitar a Abuja cewa jihohin Kaduna, Gombe, Bauchi, Kebbi, Adamawa da Taraba za su fara samun ruwan sama a safiyar Litinin, sannan a ci gaba da samun guguwar iska a yammacin ranar.
Ana kuma sa ran ambaliyar ruwa a wasu yankuna na Adamawa, Taraba da Gombe.
A yankin tsakiyar Najeriya, za a samu ruwan sama a jihohin Niger, Kogi, Kwara, Abuja da Benue, yayin da a kudanci za a samu ruwan sama a Ekiti, Ondo, Rivers, Akwa Ibom da Cross River.
NiMet ta gargaɗi direbobi da su guji tuƙa motoci yayin ruwan sama mai tsanani, sannan ta shawarci manoma da su guji yayyafa taki ko magungunan kashe kwari kafin sauƙar ruwan sama.
Haka kuma hukumar ta buƙaci kamfanonin jiragen sama da su riƙa samun sahihan rahotannin yanayi na filayen jiragen da za su sauƙa ko tashi domin tsara ayyukansu yadda ya dace.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook