Najeriya ta ƙaryata Trump bisa zargin cewa Kiristoci na fuskantar barazana a ƙasar

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ƙaryata iƙirarin shugaban Amurka, Donald Trump, na cewa Kiristoci na fuskantar barazana ta kisa da tsanantawa a Najeriya.

A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Waje ta fitar yau Asabar, gwamnatin ta ce kalaman Trump “ba su dace da gaskiyar halin da ake ciki ba” kuma “ba su wakilci yanayin tsaro na ainihi” a ƙasar ba.

Sanarwar ta ce, “Gwamnatin Tarayya ta lura da kalaman shugaban Amurka Donald J. Trump, wanda ya yi zargin cewa Kiristoci da dama na mutuwa a Najeriya, tare da neman a sanya ƙasar cikin jerin ƙasashen da ke keta ƴancin addini. Amma wannan ba shi ne halin da ake ciki ba, domin ƴan Najeriya na rayuwa tare cikin zaman lafiya.”

TIMES HAUSA ta tattaro cewa ma’aikatar ta jaddada cewa gwamnati tana bin doka wajen kare rayuka da ƴancin addini na kowane ɗan ƙasa, tare da tabbatar da zaman lafiya tsakanin mabiya addinai daban-daban.

A cewar sanarwar, “A ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Najeriya za ta ci gaba da yaƙi da ta’addanci da ƙarfafa zaman lafiya tsakanin addinai.”

Gwamnatin ta kuma ce za ta ci gaba da yin aiki tare da gwamnatin Amurka domin inganta fahimta da haɗin kai kan haƙiƙanin matsalolin tsaro da ci gaban zaman lafiya.

In za a iya tunawa, Trump ya sanar da shirin sake sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ke fuskantar barazana ga ƴancin addini, kamar yadda aka yi a shekarar 2020.

Sai dai gwamnatin Joe Biden ta cire sunan Najeriya daga jerin a 2021, bisa hujjar cewa ƙasar tana ci gaba da inganta tsarin kare addinai a cikinta.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Leave A Reply

Your email address will not be published.