Gwmnati ta rage kuɗin kujerar Hajji na 2026, akwai banbanci tsakanin yankunan Najeriya

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta fitar da sabon farashin kujerar aikin Hajji na shekarar 2026, inda ta rage kuɗin da za a biya da kusan naira dubu 200 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

Rahoton da wakilinmu ya tattaro daga wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Sani Shafii, ya fitar ya nuna cewa, alhazai daga yankin Maiduguri–Yola (wanda ya haɗa da Jihohin Yobe, Borno, Adamawa da Taraba) za su biya ₦8,118,333.67, maimakon ₦8.3m da suka biya bara.

Sauran jihohin Arewa za su biya ₦8,244,813.67, yayin da jihohin Kudu za su biya N8,561,013.6, duk da cewa a bara sun biya sama da haka.

Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Sale Usman, ya bayyana cewa an cimma wannan matsaya ne bayan tattaunawa da shugabannin jihohi da kuma amincewar Gwamnatin Tarayya.

Ya kuma yi kira ga dukkan masu niyyar zuwa Hajji su tabbatar sun biya cikakken kuɗin kafin ranar 31 ga Disamba, 2025.

Haka zalika, NAHCON ta rattaba hannu kan yarjejeniya da kamfanonin masu ba da kulawa a ƙasar Saudiyya, ciki har da Mashareeq Al-Zahabiyya da kuma Daleel Al-Ma’aleem, domin tabbatar da sauƙin gudanar da aikin Hajjin bana.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Leave A Reply

Your email address will not be published.