Misra ta shirya buɗe babban gidan tarihi na al’adunta a Cairo

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Misra ta kammala shirin buɗewa da gudanar gagarumin bikin ƙaddamar da Grand Egyptian Museum (GEM) da ke birnin Cairo – wani muhimmin mataki da ake sa ran zai farfaɗo da fannin yawon buɗe ido da tattalin arziƙin ƙasar.

TIMES HAUSA ta tattaro daga fadar shugaban ƙasar cewa shugabannin ƙasashe, sarakuna da manyan jami’an gwamnatoci ne ake sa ran zasu halarcin bikin a ranar Asabar, wanda aka bayyana a matsayin “wani abin tarihi na musamman a duniyar al’adu da wayewar ɗan Adam.”

Gidan tarihin, wanda aka gina kusa da harabar Dutsen Giza, yana da filin nunin kayan tarihi mai faɗin murabba’in mita 24,000, inda aka tara manyan kayan tarihi da abubuwan tunawa daga tsoffin daular Masar.

Ginin, wanda aka fara a 2005, ya ɗauki shekaru fiye da 20 kafin a kammala shi saboda matsalolin siyasa da rashin kwanciyar hankali.

Shugaba Abdel Fattah el-Sisi ya bayyana a shafinsa na sada zumunta cewa, “Wannan gidan tarihi zai haɗa hazaƙar tsoffin Misrawa da ƙirƙire-ƙirƙiren zamani, ya kuma zama sabon ginshiƙin wayewa da fasaha ga duniya.”

An inganta yankin da ke kusa da gidan tarihi da kuma Dutsen Giza, an shimfida tituna, an gina tashar jirgin ƙasa ta ƙarƙashin ƙasa, tare da buɗe sabon filin jirgin sama na Sphinx International Airport domin sauƙaƙa zirga-zirgar baƙi.

An ƙiyasta kuɗin aikin a sama da dala biliyan ɗaya ($1bn), inda ake sa ran zai jawo miliyoyin masu yawon buɗe ido, wanda zai taimaka wajen samar da kuɗaɗen waje da ake buƙata wajen sayen man fetur da hatsi.

A cewar gwamnatin ƙasar, an samu masu yawon buɗe ido miliyan 15.7 a 2024, kuma manufar ita ce adadin ya kai miliyan 30 a 2032.

A cewar jami’an gidan tarihi, a cikin rumfunan nuni guda 12 akwai kayan tarihi daga zamanin da har zuwa lokacin Romawa, ciki har da kayan da aka samo daga ƙabarin Sarki Tutankhamun, wanda za a nuna gaba ɗaya a karo na farko tun bayan gano shi a 1922.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Leave A Reply

Your email address will not be published.