Malaman makarantu da iyaye sun caccaki sabuwar manhajar karatun Gwamnatin Tarayya

13

Wasu malamai da iyaye sun caccaki Gwamnatin Tarayya kan sanar da sabuwar manhajar karatu ba tare da shawarar masu ruwa da tsaki ba, suna gargaɗin cewa gaggawar aiwatar da ita ka iya rage ingancin ilimi a makarantu.

Wakilinmu ya tattaro daga taron yanar gizo mai taken “Fahimtar Sabuwar Manhaja” wanda Concerned Parents and Educators Network ta shirya cewa, masu ruwa da tsaki sun bayyana damuwar cewa, matakin ya fi kama da na siyasa fiye da na ilimi.

Masani kan tarbiyar yara da shawara kan ilimi, Taiwo Akinlami, ya ce: “Idan za a fitar da manhajar karatu, ya kamata ƙungiyoyin makarantu, iyaye, malamai, har da yara su shiga ciki. Abin da muka gani kawai sanarwa ce, babu shiri.”

Masu sukar sun yi nuni da giɓin kayan aiki, musamman wajen koyar da ICT da aikin gona, inda suka ce makarantu da dama – musamman na gwamnati – ba su da kayan da ake buƙata.

Sai dai ƙwararru kamar Rhoda Odigboh sun yaba da rage yawan darussa a matsayin wani ci gaba, amma sun gargaɗi cewa rashin shirin koyar da ƙwarewar zamani na iya lalata shirin gaba ɗaya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.