Likitoci sun dakatar da yajin aiki a Najeriya, za su fitar da sabuwar matsaya a 26 ga Satumba

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Ƙungiyar Likitoci masu Koyon Aiki ta Najeriya (NARD) ta dakatar da yajin aikin gargaɗi na kwana biyar bayan yini biyu kacal, domin ba wa Gwamnatin Tarayya damar makonni biyu da ta biya buƙatunsu.

Shugaban NARD, Dr. Tope Osundara, ya shaida wa wakilin PUNCH cewa an ɗauki matakin ne don nuna alheri ga ƴan Najeriya da ke fama da matsalolin tattalin arziƙi.

“Ina tabbatar maku cewa ba mu janye buƙatunmu ba. Mun dakatar ne kawai don ba wa gwamnati dama ta aiwatar da abin da aka yi alƙawari,” in ji shi.

Buƙatun NARD sun haɗa da biyan kuɗin horon likitoci (MRTF) na 2025 ga dukkan mambobi, biyan bashin albashi na watanni biyar, da aiwatar da sabon tsarin albashi (CONMESS 2024).

Sai dai a cewar Dr. Osundara, “Abu ɗaya ne kawai gwamnati ta aiwatar, shi ne biyan MRTF ga waɗanda aka bari a baya. Har yanzu muna bin bashin kuɗaɗe da dama.”

Ƙungiyar za ta sake haɗuwa a ranar 26 ga Satumba domin yanke hukunci kan mataki na gaba idan gwamnati ta gaza biyan buƙatunsu.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Leave A Reply

Your email address will not be published.