Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Kotun Babban Birnin Tarayya da ke Abuja ta yanke wa wani malamin makaranta mai shekaru 19, Abdullahi Abbass, hukuncin ɗaurin rai da rai bayan ta same shi da laifin yin fyade da ɗalibinsa mai shekara tara – hukuncin da Hukumar Hana Fataucin Mutane (NAPTIP) ta bayyana a matsayin babbar nasara a yaƙin da take yi da cin zarafin yara.
TIMES HAUSA ta tattaro cewa, a wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na NAPTIP, Mista Vincent Adekoye, ya fitar ta shafin X a yau Asabar, an bayyana cewa Alƙalin kotun, Mai Shari’a M. Osho–Adebiyi, ne ya yanke wannan hukunci a Babbar Kotun Abuja.
Hukumar ta ce, wanda aka yanke wa hukuncin yana koyarwa ne a wata makaranta mai zaman kanta da ke Ƙaramar Hukumar Kwali, inda ya yi amfani da dabara ya jawo ɗalibin bayan kammala karatu a ranar 19 ga Maris, 2025, sannan ya yi masa fyaɗe.
“Wanda aka yanke wa hukuncin shi ne malamin ajin ɗalibin. Bayan kammala karatu, ya tura wani ɗalibi ya kira wanda abin ya shafa daga gida, daga nan kuma ya kai shi inda yake zaune sannan ya yi masa fyaɗen,” in ji sanarwar.
Rahotanni sun nuna cewa, bayan lamarin, yaron ya sanar da mahaifiyarsa, wanda hakan ya kai ga kamawa da gurfanar da Abbass a gaban kotu kan laifuka biyu – fyaɗe da cin zarafin jima’i.
A ranar 29 ga Oktoba, 2025, kotu ta same shi da laifi bisa tanadin Sashe na 2 na Dokar Hana Cin Zarafin Mutane ta 2015, wadda ta tanadar da hukuncin ɗaurin rai da rai.
Shugabar NAPTIP, Hajiya Binta Adamu Bello, ta jinjinawa kotun da sauran abokan haɗin gwiwa bisa yadda suka tabbatar da hukuncin.
“Wannan hukunci na tarihi ne da ya dace da girman laifin. Za a saka sunan wannan mutum a cikin Rijistar Masu Laifin Fyaɗe ta ƙasa domin zama izina ga sauran masu irin wannan hali,” in ji ta.
Ta kuma bayyana cewa, saurin gudanar da bincike da gurfanar da wanda aka kama ya nuna jajircewar hukumar wajen yaƙi da fyaɗe da sauran nau’o’in cin zarafin jima’i a faɗin Najeriya.
Binta Bello ta yaba da gudunmawar rundunar ƴan sanda, tana mai cewa, hukumar ba za ta gajiya ba wajen tabbatar da cewa masu laifin fyaɗe sun fuskanci hukunci.
TIMES HAUSA ta kuma tattaro daga rahoton PUNCH Online na 19 ga Yuni, 2025, cewa wani malami, Pascal Ofomata mai shekara 34, shi ma kotu ta yanke masa hukuncin shekaru 12 a gidan yari bayan samunsa da laifin yin lalata da ɗalibinsa mai shekara 11 a St. Christopher’s Junior Seminary, Onitsha, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Peace Otti na Kotun SGBV da ke Awka, Jihar Anambra.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook