Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Babbar kotun tarayya dake Abuja ta ƙi amincewa da buƙatar da tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya gabatar domin hana jam’iyyar PDP gudanar da gangamin ƙasa da aka shirya a Ibadan, Jihar Oyo, a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwambar nan.
TIMES HAUSA ta tattaro cewa Lamido, wanda ya mulki jihar daga 2007 zuwa 2015 a ƙarƙashin PDP kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka jam’iyyar a ƙasa, ya nemi a dakatar da taron har sai an saurari ƙarar da ya shigar.
Lauyansa, babban lauyan Najeriya Jeph Njikonye (SAN), ne ya gabatar da buƙatar a gaban Mai Shari’a Peter Lifu, inda ya roƙi kotun ta bayar da umarnin wucin-gadi.
Sai dai kotun ta umarci PDP da hukumar INEC su bayyana hujjoji cikin awanni 72 domin nuna dalilin da zai sa kada a amince da buƙatar tsohon gwamnan.
Alƙalin ya ɗage shari’ar zuwa ranar 6 ga watan Nuwamba domin ci gaba sauraro.
TIMES HAUSA ta fahimci cewa wannan hukunci ya zo ne a rana guda da wata kotu daban ta bayar da umarnin dakatar da gangamin jam’iyyar.
A cikin takardar ƙarar da Lamido ya shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/2299/2025, ya buƙaci kotu ta hana PDP gudanar da gangamin ko a Ibadan ko a wani lokaci dabam har sai an gama sauraron ƙarar.
Ya ce PDP tana ƙoƙarin karya kundinta kuma hakan na iya tauye masa damar tsayawa takarar shugabancin jam’iyyar.
Mai shari’a Lifu ya ce kotu ta yi la’akari da hujjojin ɓangarorin, tare da yanke shawarar cewa sai an saurari kowa kafin a ɗauki mataki, domin tabbatar da daidaito da adalci.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook