Kotu a Bauchi ta yi watsi da buƙatar hana ICPC, EFCC da NFIU bincikar ofishin SSG

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Babbar Kotun Jihar Bauchi ta yi watsi da wata ƙara da aka shigar domin hana Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa a Ma’aikatun Gwamnati (ICPC) da hukumar EFCC da NFIU bincike kan al’amuran kuɗaɗen tsaro na Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi (SSG).

Wakilinmu ya tattaro daga sanarwar ICPC cewa, ƙarar mai lamba BA/834M/2024, wadda wasu “Concern Indigenes of Bauchi State” su tara suka shigar, ta nemi a umurci hukumar ƴan sanda ta karɓi alhakin binciken maimakon ICPC, EFCC da NFIU, bisa zargin cewa sun gaza wajen gudanar da aikinsu kan ofishin SSG da suke zargi da karkatar da kuɗaɗen jama’a.

Lauyan masu ƙara, M. J Jaldi, ya shaida wa kotu cewa wasu daga cikin ayyukan Sakataren Gwamnatin Jihar, ciki har da biyan kuɗaɗe masu yawa na hannun jari ba tare da amfani da bankuna ba, sun saɓawa dokar hana karkatar da kuɗaɗe, don haka ya kamata a bar binciken hannun ƴan sanda.

Sai dai ICPC ta yi adawa da wannan ƙara ta hanyar gabatar da ƙarin hujjoji, inda ta yi nuni da cewa masu ƙarar ba su gabatar da wani takamaiman ƙorafi ga hukumomin ba.

Haka kuma, ICPC da EFCC sun bayyana cewa masu ƙarar na ƙoƙarin yin amfani da kotu wajen hana hukumomin yin aikin da doka ta ɗora musu.

A hukuncin da Mai Shari’a F. U. Sarki ya yanke, ya bayyana cewa ikon ICPC, EFCC da NFIU wajen bincike da gurfanarwa ba ya hana ikon rundunar ƴan sanda, wanda a maimakon haka ya fi faɗi da girma.

Ya ƙara da cewa “ba hurumin wannan kotu ne ta hana hukumomi na farko zuwa na uku gudanar da aikinsu na doka ba,” don haka ya yi watsi da ƙarar baki ɗaya.

Wannan hukunci dai na nuni da cewa hukumomin yaƙi da cin hanci za su ci gaba da gudanar da ayyukansu a Bauchi ba tare da tangarɗa ba.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Leave A Reply

Your email address will not be published.