Kano ta haramta amfani da zarton inji marar izini a sare bishiyoyi, ta ɓullo da tsarin ba wa zartuna lasisi
“Ba za mu ƙyale sare itace ba don na son rai kawai – ka sare ɗaya, sai ka dasa biyu ko uku,” in ji Hon. Dakta Dahiru Muhammad Hashim, kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na Jihar Kano, yayin bayyana sabuwar dokar haramta amfani da zarton inji ba tare da izini ba da tsarin CUPF (Chainsaw Usage Permit Framework).
An bayyana wannan dokar ne a cikin jerin umarnin da aka bayar a yayin taron manema labarai a ɗakin taro na Ma’aikatar Gwamnatin Tarayya da jihohi, inda Hashim ya bayyana cewa haramcin ya samo asali ne daga Matsaya ta 20 ta Kundin Tsarin Mulki na 1999, doka ta NESREA ta 2007 da kuma Dokokin Kasancewar Muhalli na 2014.
Wannan mataki ya yi daidai da NDC 3.0 na Najeriya a fannoni na duniya.
An ƙaddamar da babban tsarin yin rajista ta komfuyuta domin masu sa ido, inda za a raba izini mai ɗauke da mafayyacin bayanai (QR code) da za a iya tantance shi a ainihin lokacin da za a yi aiki.
Hukumomi, sarakuna da masu lura da dazuka a unguwanni da ƙauyuka za su taimaka wajen tabbatar da aiwatar da dokar.
Ga jerin hukuncin da za a ɗauka ga masu karya doka:
- Tarar naira 500,000, ƙwace kayan aiki ko zaman gidan yari ga wanda ya yi amfani da zarton inji ba tare da lasisi ba;
- Tarar naira 250,000 kan kowane itace da aka sare ba tare da izini ba, sai a umarci mai aikin da ya sake dasa itatuwa da kuma ƙwace kayan aikinsa.
Tsarin CUPF ya kasu gida biyu:
- CUPF-A: Lasisi ne ga ɗimbin masu aiki da zartunan inji, ana sabunta shi shekara-shekara, kuma ana mannawa zarton injin wata lamba ta Ma’aikatar.
- CUPF-B: Izini ne da ake buƙata don sare ko gyara itace – ko a fili ne ko a kaɓaɓɓen wuri – ana bayar da shi bayan gwajin jami’an daji.
An bayyana cewa, kuɗaɗen neman izinin za su tallafawa shirye-shirye na dasawa da ƙarfafa yanayi mai jure illa daga gurɓacewar muhalli a jihar.
Kwamishinan ya kuma yi kira ga shugabannin al’umma, ƙananan hukumomi, makarantu da ƙungiyoyin addini su taka rawa wajen aiwatar da wannan doka, “Muna fatan makarantu su dakatar da sare itatuwa ba tare da izini ba; shugabannin ƙananan hukumomi su kare wurare da aka tanada. Limamai da shugabannin gargajiya su wayar da kan al’umma game da illolin lalacewar muhalli.”
Har ila yau, hukumar sarakunan Kano da shugabannin ƙauyuka za su taimaka wajen lura da kuma bayar da rahoton duk wani kutsen doka a mataki na farko.
A ƙarshe, Dr. Hashim ya jaddada cewa, “Muna kira ga duk masu zartunan inji, hukumomi, ƙungiyoyi da kuma ƴan ƙasa – ku bi wannan doka. Ku nemi izini kafin fara aiki. Ku yi rijista. Ku dasa itatuwa da yawa. Mu bar Kano koriya ga zuriyar mu ta gaba.”