Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Hukumar JAMB ta bayyana cewa ta gano ɗaukar ɗalibai 2,658 da aka yi ba bisa ƙa’ida ba a wasu jami’o’i, kwalejoji, da makarantun fasaha 17 a lokacin shekarar karatu ta 2024/2025.
Wannan na zuwa ne yayin da jami’o’in gwamnati suka kammala shirin karɓar daliban sabon zangon karatu na 2025/2026 a ranar Juma’a.
Rahoton da TIMES HAUSA ta samo daga sakamakon binciken hukumar ya nuna cewa jami’ar Abubakar Tafawa Balewa University (ATBU) ce ta fi da ɗaukar haramtattun ɗaliban har 1,847, sai Jami’ar Jihar Osun (492), Abubakar Tatari Ali Polytechnic (148), da sauran makarantu da suka haɗa da Jami’ar Calabar, Michael and Cecilia Ibru University, Redeemer’s University, da Pan-Atlantic University.
JAMB ta bayyana cewa duk wata karɓar ɗalibai da aka yi ba ta hanyar tsarin Central Admissions Processing System (CAPS) ba ana ɗaukarta a matsayin haramtacciya.
Hukumar ta jaddada cewa an samar da CAPS a 2017 domin tabbatar da gaskiya da adalci a tsarin karɓar dalibai, tare da ba da damar tantancewar da dalibai za su samu ko ƙin amincewa da guraben karatun da aka ba su.
Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta yi gargaɗin cewa, jami’o’i ko jami’an da aka samu da hannu a irin wannan harƙalla za su fuskanci matakin hukunci.
JAMB ta kuma tunatar da ɗalibai cewa duk wanda ya karɓi gurbin karatu ba ta hanyar CAPS ba na iya rasa cancantar shiga aikin NYSC, bayan kammala karatu.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook