INEC ta yi magana kan sanarwar ɗaukar ma’aikata a hukumar, ta gargaɗi jama’a
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta gargaɗi jama’a da su yi watsi da wata sanarwa ta bogi da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta cewa hukumar tana ɗaukar ma’aikata.
A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X ranar Laraba, ta ce an ƙirƙiri wani shafin bogi mai suna inecrecruitment.com.com don yaudarar jama’a.
“Ba mu da irin wannan shafi, kuma ba mu fara ɗaukar ma’aikata ba. Jama’a su yi hattara kada su faɗa tarkon masu yaudara,” in ji sanarwar.
Hukumar ta ƙara jaddada cewa ba ta da wani shirin ɗaukar sabbin ma’aikata a yanzu.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook