INEC ta tantance ƙungiyoyi 14 daga cikin 171 don ci gaba da neman rajistar zama jam’iyyun siyasa

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanar da cewa ƙungiyoyi 14 daga cikin 171 da suka nemi rajista sun tsallake matakin farko na tantancewa domin zama jam’iyyun siyasa.

Sanarwar da aka fitar ranar Alhamis, 11 ga Satumba 2025, wacce Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Masu Zaɓe na INEC, Kwamishina Sam Olumekun ya sanya wa hannu, ta ce an yanke wannan hukunci ne a taron yau da kullum na hukumar.

Wakilinmu ya samu labari cewa dukkan buƙatun an tantance su ne bisa ga tanade-tanaden Sashe na 222 na Kundin Tsarin Mulki na 1999 (wanda aka yi wa gyara), da Sashe na 79 na Dokar Zaɓe ta 2022, da kuma dokoki da ƙa’idojin INEC na shekarar 2022.

Daga cikin ƙungiyoyi 171 da suka nema, 157 sun kasa cika sharuɗɗan farko, yayin da 14 suka samu nasara.

An wallafa sunayen ƙungiyoyin da suka tsallake a shafin yanar gizo na INEC da sauran hanyoyin sadarwar hukumar.

Sunayen ƙungiyoyin da suka tsallake sun haɗa da:

  • African Transformation Party (ATP)
  • All Democratic Alliance (ADA)
  • Advanced Nigeria Congress (ANC)
  • Abundance Social Party (ASP)
  • African Alliance Party (AAP)
  • Citizens Democratic Alliance (CDA)
  • Democratic Leadership Alliance (DLA)
  • Grassroots Initiative Party (GRIP)
  • Green Future Party (GFP)
  • Liberation People’s Party (LPP)
  • National Democratic Party (NDP)
  • National Reform Party (NRP)
  • Patriotic Peoples Alliance (PPA)
  • People’s Freedom Party (PFP)

INEC ta gayyaci shugabanni na wucin-gadi na waɗannan ƙungiyoyi zuwa taro a babban ofishinta dake Abuja a ranar Laraba, 17 ga Satumba 2025 da misalin ƙarfe 11 na safe.

Olumekun ya bayyana cewa hukumar ba za ta tsaya ga bayanan da aka saka a intanet kawai ba, za ta kuma gudanar da bincike kai tsaye domin tabbatar da sahihancin bayanan da ƙungiyoyin suka gabatar.

Ya nanata cewa rajistar jam’iyyun siyasa aiki ne da doka ta amince da shi a kowane lokaci, don haka INEC za ta ci gaba da karɓa da kuma tantance sabbin buƙatu da suka cika sharuɗɗan doka.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Leave A Reply

Your email address will not be published.