Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta bayyana shirinta na gurfanar da wani mutum mai suna Alkazim Kabir, wanda aka fi sani da “Abbati Kabiru Abuwa,” bisa tuhumar zamba da ta kai kusan naira miliyan 14.
Rahotannin da wakilinmu ya tattara sun nuna cewa, an kai ƙorafe-ƙorafe da dama kan mutumin, wanda ake zargi da yin amfani da sunayen jami’an gwamnati da ƴan majalisa don damfarar mutane.
Binciken ICPC ya gano cewa Kabir ya sha kwaikwayon masu muƙamai a fadar shugaban ƙasa da mataimakin shugaban ƙasa, yana karɓar kuɗi daga mutane bisa sunan taimako.
A wani lokaci, ya karɓi dala $3,300 da Riyal 1,620 daga mutane biyu, yana iƙirarin cewa shi jami’in gwamnati ne.
Har ila yau, an gano cewa yayin tafiya zuwa Saudiyya, ya karɓi aron Riyal 11,000 daga wani, sannan ya aika masa da shaidar ƙarya ta banki da ke nuna ya biya bashin.
Haka kuma ya aika da shaidar ƙarya ta naira miliyan 3.2 ga wani dillalin safarar jirage da ya shirya masa wata tafiya.
Hukumar ta tabbatar cewa ta kammala shigar da ƙara a kotu, kuma za a fara shari’ar da zarar an ware alƙali mai kula da shari’ar.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook