ICPC ta yi nasarar samun hukuncin ɗaurin shekaru ga wani tsohon daraktan da ya yi zambar miliyoyin nairori
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa tsohon Daraktan Kuɗi da Gudanarwa na Abuja Metropolitan Management Council (AMMC), Garuba Mohammed Duku, hukuncin shekara 24 a gidan yari bisa laifin zamba da almundahanar kuɗi har naira miliyan 318 kamar yanda ICPC ta bayyana.
Binciken Hukumar ICPC ya gano cewa, tsakanin shekarar 2012 zuwa 2013, Duku ya karkatar da naira miliyan 318.25 daga asusun AMMC zuwa nasa asusun a bankin Fidelity.
An gano ya raba kuɗin zuwa manyan sassa kamar naira miliyan 56.25, naira miliyan 71, naira miliyan 53, naira miliyan 54, naira miliyan 46, da naira miliyan 36.3.
A cewar ICPC, Duku ya yi amfani da waɗannan kuɗaɗen wajen hada-hadar da ba ta gwamnati ba, kuma ba shi da wata hujja ta gaskiya da ke nuna cewa ya tura kuɗin ga manyansa.
Alƙalin kotun, Mai Shari’a James Omotosho, ya bayyana cewa hujjojin ICPC sun tabbatar da laifinsa ba tare da wata shakka ba, sannan ya yanke masa hukuncin shekaru huɗu a kowane daga cikin tuhume-tuhume guda shida — ko kuma ya biya tara kwatankwancin naira biliyan 1.6.
ICPC ta ce wannan hukunci hujja ce ta ƙudurin gwamnati wajen hukunta masu ci da rashawa da cin amanar al’umma.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook