ICPC ta bankaɗo ayyuka 1,440 da kuɗinsu ya kai naira biliyan 271 a Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa a Ma’aikataun Gwamnati (ICPC) ta bayyana cewa ta bankaɗo tare da bibiyar ayyuka 1,440 da darajarsu ta kai naira biliyan 271.054 a cikin shekaru biyu da suka gabata, a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.
Wakilinmu ya tattaro daga jawabin shugaban ICPC, Dr Musa Adamu Aliyu, SAN, a wajen wani taro da aka yi da manema labarai daga shiyyoyin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas a Kano, ranar Alhamis.
Ya bayyana cewa a Arewa maso Gabas an bibiyi ayyuka 767 da kuɗinsu ya kai naira biliyan 112.737, yayin da a Arewa maso Yamma aka bibiyi ayyuka 673 da darajarsu ta kai naira biliyan 158.317.
A cewarsa, wannan nasara ta samu ne sakamakon yadda ƴan jarida da ƴan kasa ke tona asirin ayyukan da aka fara a bar su a banza.
Haka kuma, hukumar ta ƙwato naira biliyan 7.269 da dala miliyan 1.066 a Arewa maso Yamma, tare da naira miliyan 43.335 a Arewa maso Gabas.
ICPC ta kuma ƙwace gine-gine 14, filaye 25 da gonaki uku a Arewa maso Yamma.
Dr Musa ya yi kira ga majalisar dokoki ta tarayya da ta gaggauta amincewa da ƙudirin kwarmato ‘Whistleblower Bill’ domin kare ƴan ƙasa masu bayar da bayanai.
Ya kuma buƙaci ƴan jarida da su ƙara zage damtse wajen binciken gaskiya, ba tare da yin watsi da amincewar jama’a ga yaƙin da ake da cin hanci da rashawa ba.