Hukumar Hana Cin Hanci ta Jigawa ta ƙwato sama da naira miliyan 200, ta warware ƙorafe-ƙorafe

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Hukumar Karɓar Korafi da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Jigawa (PCACC) ta bayyana cewa ta ƙwato sama da naira miliyan 200 daga cikin korafe-korafen da jama’a suka shigar, tun bayan da aka kafa ta a farkon shekarar 2024.

Wakilinmu ya rawaito cewa mai magana da yawun hukumar, Yusuf Sulaiman ne ya bayyana hakan a hira da Freedom Radio ranar Laraba, inda ya ce cikin ƙorafe-ƙorafe 300 da aka shigar, an warware kusan 200.

Yusuf ya bayyana cewa nasarar ta biyo bayan haɗin kai daga jama’a, inda ake samun bayanai masu sahihanci da suka taimaka wajen gano jami’an gwamnati da kuma ƴan kasuwa da ake zargi da almundahana.

Ya buƙaci jama’a da su ci gaba da bayar da rahoto kan duk wani abu da ya saɓawa doka.

An kafa hukumar ne ƙarƙashin jagorancin Gwamna Umar Namadi, domin yaƙar cin hanci da tabbatar da gaskiya a gudanar da mulki a jihar.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Leave A Reply

Your email address will not be published.