Hukumar Alhazai ta Jigawa ta sake jaddada ranar ƙarshe ta biyan kuɗin aikin Hajjin baɗi, saura ƴan kwanaki kaɗan
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta shawarci dukkan masu niyyar zuwa aikin Hajji a shekarar 2026 da su gaggauta kammala biyan kuɗaɗen su kafin ranar 8 ga watan Oktoba 2025.
Wakilinmu ya tattaro cewa Darakta Janar na hukumar, Alhaji Umar Labbo, ne ya bayyana haka a lokacin hira da manema labarai a ofishin hukumar da ke Dutse, babban birnin jihar, ranar Laraba.
Ya bayyana cewa hukumar ta shirya wata bita ta musamman domin horar da jami’an mahajjata da na sassa domin inganta walwala da magance ƙalubalen da ke tunkarar aikin Hajji.
Labbo ya jaddada cewa wannan bita na da matuƙar muhimmanci duba da ci gaba da biyan kujerun Hajji, tare da jaddada muhimmancin biyan kuɗin a kan lokaci domin guje wa cunkoso da rikice-rikice a ƙarshe.
Ya ƙara da cewa Jigawa ta samu kujerun Hajji sama da 1,600 daga Hukumar Kula da Ayyukan Hajji ta Ƙasa (NAHCON), kuma shirye-shirye suna tafiya yadda ya kamata domin gudanar da aikin cikin nasara.
A cewarsa, tsarin gudanar da ayyukan bana ya fi na bara kyau, duba da darussan da aka koya daga baya.
Daraktan ya yaba da goyon bayan Gwamna Umar Namadi wanda ya ce ya ƙara ƙarfafa aikin hukumar.
“Kwamitin na da tabbacin cewa da waɗannan matakai da kuma goyon bayan gwamnati, alhazan Jigawa za su samu kwanciyar hankali da sakamakon hajji mai albarka a 2026,” in ji shi.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook