Hon. Rossi zai gina rijiyoyin burtsatse a faɗin Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu don rage wa jama’a wahalar ruwan sha

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Rahotannin da TIMES HAUSA ta tattaro daga ofishin ɗan majalisar dokokin Jihar Jigawa mai wakiltar mazaɓar Birnin Kudu, Honarabul Muhammad Kabir Ibrahim Yayannan (Rossi), sun tabbatar da cewa, ɗan majalisar ya ƙaddamar da shirin gina rijiyoyin burtsatse na tuƙa-tuƙa guda goma sha ɗaya (11) a sassa daban-daban na ƙaramar hukumar Birnin Kudu, domin rage wa jama’ar yankin wahalar samun ruwan sha mai tsafta.

Wannan aikin, na daga cikin shirin raya al’umma da Honarabul Rossi ke aiwatarwa, musamman ta fuskar kula da walwalar jama’a da ci gaban ƙauyuka.

Wakilinmu ya fahimci cewa, aikin zai gudana ne a ƙarƙashin kulawar hukumar da ke kula da ruwa da ayyukan ci gaba na majalisar, tare da haɗin gwiwar shugabannin yankuna.

A cewar takardar bayanin ayyukan da ofishinsa ɗan majalisar ya fitar, wuraren da za a gina rijiyoyin sun haɗa da Juwan Kwari da Babban Titi Markaz Transformer a gundumar Kangire, Badingu a Surko, Tsangaya Alaramma Malam Dan. Jajeri, Agarazuwa Massalacin Masjudul Ibadurrahman Bayan Masmawa Primary School, da Dutsin Maidodo a gundumar Birnin Kudu.

Sauran wuraren sun haɗa da Yarma a Unguwar ’Ya, Kwadage a Kantoga, Iggi a Yalwan Damai, Tsallakawa a Sundumina, da kuma Guna’an Damau a Wurno.

Da yake ƙarin haske game da waɗannan ayyuka, Honarabul Rossi ya bayyana cewa, “Wahalar samun ruwa mai tsafta a yankunanmu na Birnin Kudu ta daɗe tana damun jama’a. Wannan dalili ne ya sa muka ɗauki matakin samar da rijiyoyin tuka-tuka guda goma sha ɗaya don rage wannan matsala.”

Ya ƙara da cewa, aikin ba wai kawai zai samar da ruwa ba ne, har ma zai taimaka wajen inganta lafiyar jama’a, rage cututtuka masu alaƙa da gurɓataccen ruwa, da ƙarfafa tattalin arziƙin iyalai da ke dogaro da noma da kiwo.

Wakilinmu ya gano cewa, shirin ya samo asali ne daga rahotannin da aka tattara daga shugabannin ƙauyuka da jami’an kula da walwalar jama’a, inda aka gano cewa matsalar ruwa ta fi tsanani a yankunan da ke da nisa daga babbar cibiyar ƙaramar hukumar.

A wani ɓangare na jawabin nasa, ɗan majalisar ya roƙi jama’ar da za su amfana da rijiyoyin da su ba da cikakken haɗin kai wajen kiyayewa da kula da rijiyoyin bayan an kammala aikin, domin tabbatar da ɗorewarsu.

“Ina kira ga dukkan al’umma su ɗauki wannan aiki tamkar nasu ne. Ɗorewar rijiyoyin ya dogara da yadda jama’a za su kula da su da gaskiya da amanar jama’a,” in ji shi.

Rossi, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa kan Harkokin Mata da Ci gaban Zamantakewa, ya bayyana cewa, wannan aikin ba zai tsaya nan ba, domin akwai sabbin shirye-shirye na samar da ƙarin rijiyoyi, gyaran hanyoyi da tallafawa makarantu da cibiyoyin lafiya a cikin shekara mai zuwa.

Wasu mazauna Birnin Kudu da wakilinmu ya zanta da su sun bayyana farin cikinsu kan wannan ci gaba, inda suka bayyana cewa, rashin samar da ruwa mai tsafta shi ne ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ke hana ci gaban yankin.

Wani mazaunin Yalwan Damai ya ce, “Ruwan rijiyar tuƙa-tuƙa zai taimaka sosai, musamman yanzu da lokacin damina ke ƙarewa. Wannan aikin babban taimako ne ga jama’ar Birnin Kudu.”

Rahotanni daga ofishin ɗan majalisar sun kuma nuna cewa, an riga an kammala shirin fara aikin da zarar an gama binciken ƙasa da tantance wuraren da za a huda rijiyoyin.

A cewar wakilinmu, wannan mataki ya ƙara tabbatar da cewa, Honarabul Rossi na ci gaba da nuna kishin yankinsa ta hanyar aiwatar da ayyuka masu tasiri ga jama’a, musamman a fannin ruwan sha da walwalar al’umma.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Leave A Reply

Your email address will not be published.