Hasashen samun ruwan sama da guguwar iska a sassa daban-daban na Najeriya na yau Lahadi daga NiMet

44

Hukumar Hasashen Yanayi ta Ƙasa (NiMet) ta fitar da hasashen cewa ruwan sama mai ɗauke da guguwa zai ratsa sassa daban-daban na Najeriya a ranar Lahadi, 7 ga Satumba, 2025.

Wakiliyarmu, Maryam Ayuba Auyo ta gano daga hasashen hukumar cewa yankin arewacin Najeriya na fuskantar manyan sauye-sauyen yanayi.

Ana sa ran samun guguwar iska mai ɗauke da ruwan sama mai matsakaicin yawa a safiyar Lahadi a Kebbi, Sokoto, Taraba, Borno, Yobe, da Adamawa, yayin da da rana da kuma dare ake sa ran samun guguwar iska da ruwan sama a Borno, Bauchi, Gombe, Zamfara, Kebbi, Katsina, Kaduna, Taraba, da Adamawa.

A yankin tsakiyar ƙasar kuma, ana sa ran samun guguwar iska mai tafi da ruwan sama marar yawa da safe a wasu sassan Niger da Kwara, sannan daga baya da rana zuwa dare ana sa ran samun ruwan sama mai matsakaicin yawa a Nasarawa, Niger, Plateau, Kogi, Kwara, Benue, da Babban Birnin Tarayya (FCT).

A kudancin Najeriya, ana sa ran samun gajimare da ruwan sama jifa-jifa a Oyo, Cross River, da Akwa Ibom a safiyar Lahadi, yayin da ake sa ran samun ruwan sama a shima jifa-jifa daga rana zuwa dare a Oyo, Ondo, Osun, Ekiti, Edo, Delta, Enugu, Ebonyi, Abia, Imo, Anambra, Bayelsa, Rivers, Cross River, da Akwa Ibom.

NiMet ta gargaɗi jama’a da su riƙa yin taka-tsantsan a yayin guguwar iska, tana mai jaddada cewa iska mai ƙarfi na iya rage hangen nesa, ta kuma sa hanyoyi su shiga haɗari, ta kuma janyo matsaloli ga ayyukan waje.

Hukumar ta yi kira ga al’ummomi da ke yankunan da ambaliya ke iya shafar su da su kasance cikin shiri, tana mai jan hankalin jama’a cewa “shirye-shirye na taimakawa wajen kare rayuka da dukiyoyi a irin wannan lokaci na yawaitar ruwan sama.”

Leave A Reply

Your email address will not be published.