Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bayar da tallafin naira miliyan biyu ga wasu ɗalibai ƴan Maigatari da suka nuna bajinta a taron “Gwamnati da Jama’a” da aka gudanar a ƙarshen makon da ya gabata.
Wakilinmu ya tattaro cewa ɗaliban mata daga aji biyu (SS2) na makarantar Federal Government College, Kiyawa, sun samu karramawa a gaban majalisar zartarwa ta jiha, inda gwamnan ya ɗauki nauyin karatunsu har zuwa jami’a.
Haka kuma, kamfanin Dan Modi Foods Processing Ltd ya ɗauki alƙawarin ci gaba da tallafa mu su har bayan gwamnatinsa.
Bugu da ƙari, gwamnan ya bayar da naira dubu 500 ga malamin da ya jagoranci ɗaliban zuwa gidan gwamnati.
Mambobin majalisar zartarwa suma sun ba da gudunmawarsu, inda jimillar tallafin ta kai kusan naira miliyan huɗu da rabi.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook