Gwamna Bago ya kare dokar bibiya da tabbatar da amincewa da kalar wa’azi kafin a yi shi a Jihar Neja
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago, ya kare sabuwar dokar da ke buƙatar malaman addini su gabatar da huɗubarsu kafin su hau mumbari, yana mai cewa manufar ita ce kare zaman lafiya da tsaron jama’a, ba takura wa ƴancin addini ba.
A wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin Politics on Sunday na TVC, Bago ya ce, “Ban haramta wa’azi ba. Amma kowa zai yi wa’azi, sai ya kawo littafinsa domin a duba. Haka ake yi a ƙasashe kamar Saudiyya. Ba za mu bari a yi wa’azin da zai tayar da fitina ko ya yi wa gwamnati kutse ba.”
A baya-bayan nan, Hukumar Harkokin Addini ta Jihar Neja ta sanar da cewa dukkan malaman addini za su nemi lasisi daga gwamnati cikin watanni biyu kafin su ci gaba da yin wa’azi.
Sai dai hakan ya jawo cece-kuce, yayin da Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen Neja ta ce wannan mataki bai shafi Kiristoci ba, tana mai bayyana shi a matsayin tsarin takardar shaidar wa’azi (Da’awah Registration Form) domin tabbatar da zaman lafiya.
Hukumar Harkokin Addini ta jihar ta ce manufar ita ce “inganta haɗin kai da daidaiton addini a faɗin jihar, tare da tabbatar da cewa duk wani wa’azi ya dace da zaman lafiya.”
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook