Fubara ya yi jawabi ga al’ummar Rivers karo na farko bayan ƙarewar dokar ta-ɓaci a jihar, ya gode wa Tinubu

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Wakilinmu ya tattaro cewa Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya yi jawabi ga jama’ar jiharsa a ranar Juma’a, 19 ga Satumba, 2025, bayan ƙarshen wa’adin watanni shida na dokar ta-ɓaci da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya tun a ranar 18 ga Maris.

A cikin jawabin da aka watsa a gidajen rediyo da talabijin, Gwamna Fubara ya bayyana cewa dokar ta-ɓacin ta kasance wani ƙalubale mai girma ga jihar, amma ya zaɓi yin biyayya domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban Rivers.

Ya ce, “Mun fuskanci wahala da ƙalubale, amma mun amince da matakin Shugaban Ƙasa saboda babu sadaukarwa da ta fi muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan Rivers. Ina kuma gode wa Shugaban Ƙasa bisa ƙoƙarinsa na sasanta rikicin siyasar da aka shiga.”

Fubara ya ƙara da cewa dukkan shugabannin siyasa, ciki har da tsohon gwamna Nyesom Wike da ƴan majalisar dokokin jihar, sun amince su rufe babin rikici tare da ci gaba da yin sulhu.

Ya ja hankalin ƴan siyasa da shugabanni da cewa lokaci ya yi da za a sanya banbance-banbancen siyasa a gefe, a mayar da hankali kan cigaban al’umma.

“Muna fatan zaman lafiya da muka runguma yanzu zai ɗore. Zan ci gaba da yin aiki tare da majalisar dokokin jihar domin mu dawo da harkokin mulki da aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa da muka fara,” in ji shi.

Gwamnan ya gode wa jama’ar Rivers bisa haƙuri da juriyar da suka nuna tsawon lokacin dokar ta-ɓacin, tare da tabbatar musu cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da haɗa kai da kowa.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Leave A Reply

Your email address will not be published.