Fadar Shugaban Ƙasa ta mayar da martani kan gargaɗin Atiku na yiwuwar samun juyin-juya-hali a Najeriya
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Fadar Shugaban Ƙasa a ranar Litinin ta yi watsi da gargaɗin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, cewa yunwar da ake fama da ita a ƙasar na iya haddasa tashin hankali makamancin irin juyin juya halin Faransa na 1789.
A wata sanarwa da mai ba Shugaban Ƙasa shawara na musamman, Bayo Onanuga, ya fitar da yammacin Litinin, fadar ta bayyana kalaman Atiku a matsayin “magana mai sauƙi wacce ba ta da alaƙa da ainihin halin da al’ummar Najeriya ke ciki.”
Atiku, wanda ya sha kaye a hannun Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2023, ya bayyana cewa hauhawar yunwa na iya jawo fushin jama’a irin juyin juya halin Bolshevik a Rasha a 1917.
Sai dai fadar shugaban ƙasa ta ce ƙididdigar Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) na nuna adadi mafi inganci, inda aka bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki ta ragu na tsawon watanni biyar a jere, tare da samun gagarumar riba a cinikayyar ƙasa da ƙasa, inda fitar da kayayyakin da ba na mai ba ya kusa daidaita da mai a kashi 48 bisa 52.
Wakilinmu ya tattaro daga sanarwar Onanuga cewa, asusun ajiya na ƙasa ya ƙaru zuwa kusan dala biliyan 42 daga biliyan 32 lokacin da Tinubu ya hau mulki, bayan biyan bashin da ya kai sama da dala biliyan 7, ciki har da dala miliyan 800 da ake bin ƙasar daga kamfanonin jiragen sama na waje.”
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Jihohi yanzu suna iya biyan albashi da haƙƙoƙin ma’aikata a kan lokaci, tare da samun kuɗin gina ayyukan raya ƙasa – abin da ba a saba gani a baya ba. Najeriya tana tafiya daidai da kwaskwarimar Shugaba Tinubu.”
Fadar ta zargi Atiku da PDP da yin watsi da waɗannan nasarorin, tare da mayar da hankali kan “labaran tsoro” da suka samo asali daga mulkinsu a baya.
Shugaba Tinubu, wanda ya shafe shekara biyu da watanni biyar a mulki, ya gudanar da manyan sauye-sauyen tattalin arziƙi ciki har da cire tallafin man fetur da daidaita tsarin musayar kuɗi.
Masu sukar gwamnati dai na jaddada cewa waɗannan matakan sun ƙara matsa wa talakawa, musamman da tsadar abinci da talauci ke ƙaruwa.
Sai dai Onanuga ya dage da cewa, “Muna alfahari da cigaban da ake samu ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu. Atiku da magoya bayansa na iya yin watsi da waɗannan abubuwa, amma ƴan Najeriya suna gani suna kuma jin canje-canjen da ke gudana a faɗin ƙasar.”
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook