EFCC ta ritsa ƴan damfara da intanet har su 19, ta kama su tare da ƙwace kayan aikinsu

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Wakilinmu ya tattaro daga hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa, EFCC, cewa jami’anta daga ofishin Kaduna sun kama mutane 19 da ake zargi da yin damfara ta intanet a ƙaramar hukumar Lapai ta Jihar Neja.

An ce an kama su ne a ranar Juma’a, 19 ga Satumba, 2025, bayan samun sahihan bayanai da suka nuna cewa suna da hannu a ayyukan damfara ta yanar gizo.

A cewar hukumar, waɗanda aka kama sun haɗa da maza 18 da mace ɗaya.

Hukumomin EFCC sun ce sun ƙwato wata motar Honda Civic, wayoyin hannu 33, kwamfutoci biyar, janareta ɗaya, lasifikokin Bluetooth uku, farin ƙaho da wasu kayayyakin aiki daga hannunsu.

EFCC ta tabbatar da cewa ana ci gaba da bincike kuma da zarar an kammala, za a gurfanar da su a kotu domin fuskantar shari’a.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Leave A Reply

Your email address will not be published.