Duk ɗan Afirkan da zai je Burkina Faso ba sai ya biya kuɗin biza ba – Gwamnatin Ƙasar

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Gwamnatin Burkina Faso ta sanar da cire kuɗin biza ga dukkan ƴan ƙasashen Afirka, a wani mataki da ta bayyana a matsayin ƙarfafa zumuncin ƴan Afirka da kuma sauƙaƙa motsi da hulɗar kayayyaki.

BBC ta rawaito cewa Ministan Tsaro na ƙasar, Mahamadou Sana, ne ya bayyana wannan sabon tsari a ranar Alhamis, jim kaɗan bayan taron majalisar ministoci da shugaban mulkin soja na ƙasar, Kyaftin Ibrahim Traore, ya jagoranta.

“Daga yanzu, duk ɗan ƙasar Afirka da zai yi tafiya zuwa Burkina Faso ba zai sake biyan kuɗin biza ba,” in ji Sana.

Duk da haka, ya bayyana cewa matafiya za su ci gaba da yin rajista ta yanar gizo kafin shiga ƙasar.

Wakilinmu ya rawaito daga BBC cewa, ƙasashen ECOWAS na Yammacin Afirka tun tuni suna tafiya zuwa Burkina Faso ba tare da biza ba, amma wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da ake nuna shakku kan matsayin ƙasar a ƙungiyar bayan ta fice tare da Mali da Nijar tun farkon wannan shekara.

A wata sanarwa daga gwamnatin sojan, an bayyana cewa “cire kuɗin bizar ga ƴan Afirka zai kuma taimaka wajen bunƙasa yawon buɗe ido da al’adun Burkinabe, tare da inganta suna da martabar ƙasar a idon duniya.”

Traoré, wanda ya yi juyin mulki a shekarar 2022, ya sha bayyana kansa a matsayin jagoran ƴan kishin Afirka wanda ke adawa da tasirin mulkin mallaka da mamayar Yamma.

Sai dai ƙasar, kamar maƙwabtanta Mali da Nijar, na fama da matsalar ta’addancin masu iƙirarin jihadi sama da shekara goma, inda kimanin kashi 40 cikin 100 na yankunan ƙasar ba sa ƙarƙashin ikon gwamnati.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Leave A Reply

Your email address will not be published.