Dokar Harajin Tinubu: Majalisar Wakilai ta kafa kwamitin bincike, PDP ta nemi a jinkirta aiwatarwa
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook
Majalisar Wakilan Najeriya ta kafa kwamitin wucin-gadi na musamman domin binciken zargin saɓani da ke tsakanin dokokin gyaran haraji da majalisa ta amince da su da kuma kwafin dokar da aka wallafawa al’umma (gazette) da ke yawo a hukumomin gwamnati.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ƙara jinkirta fara aiwatar da sabuwar dokar harajin daga ranar 1 ga Janairu, 2026, zuwa aƙalla watanni shida na gaba.
PDP ta ce wannan buƙata ta zama dole ne sakamakon abin da ta kira canje-canjen da ba su da hurumin doka da aka ce an shigar cikin dokar bayan amincewar Majalisar Tarayya.
Shugaba Bola Tinubu kwanan nan ya rattaba hannu kan manyan dokokin gyaran haraji guda huɗu, ciki har da Dokar Harajin Najeriya, Dokar Gudanar da Haraji, Dokar Kafa Hukumar Haraji ta Najeriya, da Dokar Hukumar Haɗin Gwiwar Haraji, duk a ƙarƙashin sabuwar Hukumar Haraji ta Najeriya (Nigeria Revenue Service).
An tsara dokokin ne domin sauƙaƙa biyan haraji, faɗaɗa tushen haraji, kawar da cunkoson haraji da kuma zamanantar da tsarin tara kuɗaɗen shiga a matakan tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi.
An shirya fara aiwatar da su ne ranar 1 ga Janairu, 2026, bayan wa’adin watanni shida na wayar da kai kan dokokin.
Sai dai gyaran harajin ya ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce a faɗin ƙasar.
A ranar Laraba, Ɗan Majalisa Abdussamad Dasuki daga Jihar Sokoto ya ja hankalin Majalisar Wakilai kan zargin bambance-bambance tsakanin dokar da aka zartar da kuma wadda aka wallafa.
Dasuki ya gargaɗi cewa idan ba a ɗauki mataki ba, dokokin na iya zama marasa ingancin shari’a, kasancewar ba su samu sahalewar majalisa ba.
“Ina roƙon a kawo dukkan takardu gaban Babban Zauren Majalissar domin mu duba mu kuma gyara inda ya dace. Wannan keta Kundin Tsarin Mulki ne,” in ji Dasuki.
A zaman Majalisar na ranar Alhamis, Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya bayyana muhimmancin lamarin tare da sanar da kafa kwamitin mutum bakwai domin bincike.
“Shugabancin Majalisar ya yanke shawarar kafa kwamitin da zai binciki dukkan batutuwan da aka taso da su,” in ji Abbas, yayin da ya bayyana Mukhtar Betara a matsayin shugaban kwamitin, tare da Idris Wase, James Faleke, Sada Soli, Igariwey Iduma, Fredrick Agbedi da Babajimi Benson a matsayin mambobi.
A martaninta, PDP ta yabawa Dasuki bisa “natsuwa da jajircewa” tare da buƙatar a ƙara ɗage fara aiwatar da dokar harajin na tsawon watanni shida domin ba da damar bincike da wayar da kan jama’a.
Jam’iyyar ta gargaɗi cewa dole ne a binciki saɓanin sosai, tana mai cewa, “Najeriya na da ƴancin sanin yadda waɗannan ƙarin sashe suka shiga dokar da aka wallafa. Wannan ba batu ne da za a share shi ƙarƙashin tabarma ba.”
Buƙatar PDP ta zo ne kwana guda bayan National Opposition Movement (NOM) ta nemi dakatar da aiwatar da tsarin harajin gaba ɗaya.
Mai magana da yawun NOM, Chille Igbawua, ya ce tsarin “mai tsauri da azabtarwa ne” ga ƴan Najeriya da ke fama da talauci da tsadar rayuwa.
“Ba za ka iya harajin yunwa ba, ba za ka iya harajin talauci ba,” in ji shi.
Sai dai Gwamnatin Tarayya ta mayar da martani, inda Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tattalin Arziƙi, Tope Fasua, ya ce wasu mutane na ƙoƙarin kawo cikas ga nasarar gyaran harajin.
“Wannan tsari na kare talakawa ne, ba wai ƙara musu nauyi ba,” in ji Fasua a Abuja.
Shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Gyaran Haraji, Taiwo Oyedele, ya ce dokokin an tsara su ne domin rage wa ƴan Najeriya wahala, yayin da Darakta Janar na NOA, Lanre Issa-Onilu, ya tabbatar da cewa za a yi amfani da dukkan hanyoyin sadarwa na hukumar domin kawar da rashin fahimta game da dokokin.
TIMES HAUSA ta fahimci cewa, duk da ce-ce-kucen, gwamnatin tarayya na nan daram kan shirin fara aiwatar da gyaran harajin a ranar 1 ga Janairu, 2026, muddin majalisa ta kammala bincikenta.
Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook