CP Dahiru ya karrama sabbin waɗanda su ka sami matsayin DSP a Jihar Jigawa

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Kwamishinan Ƴan Sandan Jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ya karrama wasu jami’ai da suka samu ci gaba zuwa matsayin Deputy Superintendent of Police (DSP) a wata gagarumar liyafa da aka gudanar a Hedikwatar Rundunar Ƴan Sanda da ke Dutse.

Bikin ya samu halartar manyan jami’ai, shugabannin gargajiya, abokai da iyalan waɗanda suka samu matsayin.

A jawabin sa, CP Dahiru ya taya sabbin DSP murna, inda ya tunatar da su cewa “samun ci gaba a matsayi na nufin ƙarin nauyin aiki.”

Ya kuma ja hankalinsu da su kasance abin koyi, su ƙara dagewa wajen yaƙi da aikata laifi da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

DSP Musa Danladi, a madadin sabbin DSPs, ya gode wa IGP, hukumar Police Service Commission da CP Dahiru saboda goyon bayan da suka nuna musu, inda ya yi alƙawarin jajircewa wajen sauƙe nauyin da ya rataya a wuyansu.

Bikin ya ƙare da ɗaukar hotuna, nishaɗi da addu’a ga zaman lafiya da cigaban Jigawa da Najeriya baki ɗaya.

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Leave A Reply

Your email address will not be published.