Browsing Category
Tsaro
Bayanan tsaro da rahotanni kan tsaro a ƙasa da waje.
Ƴan Sanda sun cafke ɓarayi da ƴan fashi a Jigawa, sun gano babura da wayoyin hannu
Jami’an ƴan sanda a jihar Jigawa sun samu nasarar cafke mutane da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, ciki har da ƴan fashi, ɓarayin babura, da masu satar wayoyi, inda suka ƙwato babura uku, wayoyin hannu biyu da wuƙa daga hannun su.
!-->!-->…
A iya wata 1 a Najeriya, an kama masu laifi 1,950, an ceto 141, EFCC kuma ta ƙwato sama da naira…
Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa (NOA) ta bayyana cewa a watan Agustan 2025, ƴan sanda sun kama mutane 1,950 tare da ceto mutane 141 da a kai garkuwa da su, yayin da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci (EFCC) ta samu nasarar hukunce-hukunce 588!-->…
Rundunar ƴan sanda ta ragargaji manyan dillalan miyagun ƙwayoyi a Jigawa
Rundunar ƴan sanda ta Jihar Jigawa ta samu nasarar cafke mutane goma sha uku da ake zargin manyan dillalan miyagun ƙwayoyi ne, a wani jerin samame da ta gudanar a sassan jihar daga ranar 2 zuwa 6 ga Satumba, 2025.
Wakilinmu, Zulkifl!-->!-->!-->…
Wasu ƴan bindiga sanye da hijabi sun sace mutane 2 a Neja, yayin da sojoji suka kashe Kachalla Balla…
Wakilinmu, Bashar Aminu ya samo cewa ƴan bindiga sanye da hijabi sun sace mutane biyu a Melehe, ƙaramar hukumar Kontagora, Jihar Neja, yayin da rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar kashe sanannen shugaban ƴan fashi, Kachalla Balla, tare!-->…
Mutane 63 ne suka mutu, ciki har da sojoji, a sabon harin da Boko Haram ta kai Jihar Borno
Fushi da alhini sun mamaye Bama a Jihar Borno bayan aƙalla mutane 63, ciki har da sojoji biyar, sun rasa rayukansu a sabon harin da Boko Haram ta kai a garin Darajamal, wanda aka dawo da mazauna cikinsa kwanan nan bayan gudun hijirar!-->…
Ƙungiyar Kare Haƙƙin Bil’adama ta saki zazzafan gargaɗi kan barazanar DSS na hana amfani da manhajar…
Ƙungiyar Kare Haƙƙin Bil’adama ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya gaggauta umartar Hukumar Tsaron Ƙasa (DSS) ta janye barazanar hana X (Twitter a da) a Najeriya, suna masu cewa hakan zai zama take haƙƙin ƴancin faɗar albarkacin baki!-->…
Ƴan Bindiga sun kashe mutum takwas, sun sace uku, sun ƙone motocin sintiri a Katsina
Ƴan bindiga sun kashe mutum takwas, sun kuma ƙone motocin sintiri biyu tare da yin garkuwa da mutane uku a wani hari da suka kai ƙauyen Magaji Wando a Ƙaramar Hukumar Dandume, Jihar Katsina.
Wakilinmu Bashar Aminu ya tattaro daga!-->!-->!-->…
Ƴan Sanda sun ritsa gungun ɓarayin kayan lantarki da ke jefa ƴan Jigawa cikin duhu
Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Jigawa ta rusa wata babbar ƙungiyar masu lalata kayayyakin lantarki da ake zargin sun lalata transfomomi 15 da manyan wayoyin wuta waɗanda darajarsu ta kai miliyoyin nairori a sassa daban-daban na jihar.
!-->!-->!-->…
Wani saurayi ya yi ajalin tsohuwar budurwarsa shekaru biyu bayan rabuwarsu
Times Hausa ta sami rahoton cewa, wata matashiya, Deborah Moses, wadda aka fi sani da Deb’rah Porsche, ta rasa ranta a Lagos bayan da tsohon saurayinta, Lintex Ogale, ya kai mata hari, kusan shekaru biyu bayan ta kawo ƙarshen!-->…
Wata sabuwar cuta ta yi ajalin yara a Borno, iyayensu kuma na kwance a asibiti
An shiga jimami a ƙauyen Kukurpu da ke yankin Kwajaffa a Ƙaramar Hukumar Hawul, Jihar Borno, bayan da wasu yara huɗu ƴan gida ɗaya suka rasu a dalilin wata mummunar cuta, yayin da iyayensu ke samun kulawa a asibiti.
Zagazola Makama, mai!-->!-->!-->…