Browsing Category
Labarai
Sabbin rahotanni daga Najeriya da duniya.
Amaechi ya ce, Tinubu “Ba shi da wayo, an kayar da shi a Legas”, ya buƙaci haɗin gwiwa don kayar da…
Tsohon gwamnan Jihar Rivers kuma babban jigo a jam’iyyar ADC, Rotimi Amaechi, ya buƙaci ƴan Najeriya da su shirya yin zaɓe mai tarin jama’a a 2027 domin hana Shugaba Bola Tinubu samun wa’adi na biyu.
TIMES HAUSA ta tattaro daga taron!-->!-->!-->…
Rahoto ya fallasa yanda ƴan sanda sama da 100,000 ke bauta wa Manya a Najeriya, an bar talakawa…
Sabon rahoton da Hukumar Ba da Mafaka ta Tarayyar Turai (EUAA) ta wallafa a Nuwamba 2025 ya nuna cewa sama da jami’an ƴan sanda 100,000 a Najeriya an tura su ne domin kare manyan ƴan siyasa da fitattun mutane (VIPs), lamarin da ke rage!-->…
Gwamnati ta rage kuɗin aikin Hajji, ta sanya sabon wa’adin biyan kuɗi
Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta sanar da sabon ragi kan kuɗin aikin Hajji na 2026 ga maniyyata daga sassa daban-daban na ƙasar, matakin da ya nuna samun babban sauƙi idan aka kwatanta da kuɗin 2025.
Bayanan da Hukumar ta fitar!-->!-->!-->…
Gwamnatin Najeriya ta ce tsaro ya inganta da kashi 80%, duk da gargaɗin Biritaniya kan barazanar…
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce bayanan da ta tattara kan tsaro sun nuna ana samun ci gaba da fiye da kashi 80 cikin 100 wajen rage hare-haren ta’addanci da satar mutane a sassan ƙasar.
Wannan bayanin na zuwa ne a daidai lokacin da!-->!-->!-->…
Sojojin Najeriya sun ceto mutum 86, sun kama ƴan bindiga 29 bayan artabu da Boko Haram
Rundunar sojin ƙasa ta Najeriya ta sanar da ceto mutum 86 daga hannun masu garkuwa da mutane, tare da kama ƴan bindiga da masu taimaka musu 29 a yankuna daban-daban na Jihar Borno.
Sanarwar da kakakin Operation Hadin Kai, Sani Uba, ya!-->!-->!-->…
ASUU ta zargi Gwamnatin Tarayya da rashin bai wa ilimi muhimmanci a Najeriya
Shugaban Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU, Farfesa Chris Piwuna, ya zargi Gwamnatin Tarayya da gazawa wajen baiwa ilimi matsayinsa na muhimmin ginshiƙin ci gaban ƙasa, yana mai cewa yawancin jami’an gwamnati ba sa ɗaukar matsalolin ilimi!-->…
Ɗan Majalissar Wakilan da NNPP ta dakatar ya koma APC, Zai yi wa Tinubu aiki a 2027
Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kiru/Bebeji, Abdulmumin Jibrin Kofa, ya sanar da komawarsa jam’iyyar APC, tare da bayyana cikakken goyon bayansa ga ƙoƙarin Shugaba Bola Tinubu na neman wa’adi na biyu a 2027.
A wani taron siyasa da ya!-->!-->!-->…
Sojoji sun buɗe wuta kan ƴan sanda a Anambra bayan kammala zaɓen gwamna
Sojoji da ke bakin shingen bincike a kan titin Onitsha sun buɗe wuta kan wasu jami’an ƴan sanda da ke dawowa daga aikin zaɓe na gwamnan Anambra, abin da ya jawo fargaba a yankin a ranar Lahadi.
TIMES HAUSA ta tattaro daga Sahara!-->!-->!-->…
BBC ta bankaɗo muhimman bayanai kan zargin Amurka na “kisan ƙiyayya wa Kiristoci” a Najeriya
Binciken BBC ya gano cewa alƙaluman da jami’an gwamnatin Amurka ke amfani da su wajen zargin ana aiwatar da “kisan ƙiyayya wa Kiristoci” a Najeriya ba su da tushe da za a iya tabbatarwa.
TIMES HAUSA ta tattaro daga rahoton cewa yawancin!-->!-->!-->…
Ɗan takarar ADC a Anambra ya kira sakamakon zaɓen gwamnan jihar a matsayin abin allawadai
Ɗan takarar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a zaɓen gwamnan Anambra na 8 ga Nuwamba, John Nwosu, ya yi watsi da sakamakon zaɓen, yana mai cewa abin da ya gudana “ba zaɓe ba ne, kuma tsarin ya miƙa wuya ga ta’asar cin hanci.”
!-->!-->!-->…