Browsing Category
Labarai
Sabbin rahotanni daga Najeriya da duniya.
ADC ta bayyana ra’ayinta kan naɗa sabon shugaban INEC
Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta bayyana cewa tana kula da matakin da gwamnati ke ɗauka na naɗa Farfesa Amupitan a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), amma tana fatan zai tabbatar da sahihin!-->…
Yanzu duk wata kwangila da ba ta haura naira biliyan 20 ba kamfani ɗan Najeriya ne zai na yi –…
Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗaukar sabon tsarin fifita ayyuka wajen biyan kuɗaɗen ayyukan gine-ginen hanyoyi da kamfanin NNPCL ya bari a hannunta, domin tabbatar da ci gaba da aiwatar da su cikin inganci da daidaito da umarnin Shugaban!-->…
EFCC ta yi wa matasa nasiha, ta ce su bi shawararta ko nan gaba su yi nadama
Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya shawarci matasan Najeriya da su guji aikata damfara ta yanar gizo tare da karkatar da basirarsu wajen aikin gina ƙasa da ci gaban tattalin arziƙi.
!-->!-->!-->…
Ƴan Sanda sun cafke masu safarar miyagun ƙwayoyi da ɓarayin dabbobi a Jigawa
Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Jigawa ta sanar da cafke mutane 21 da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi tare da ɓarayin dabbobi da masu fasa-gidaje a sassa daban-daban na jihar.
Kwamishinan Ƴan Sanda na jihar, CP Dahiru Muhammad, ya!-->!-->!-->…
Shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu ya ƙaddamar da sabbin injinan ruwa domin tabbatar da samar da…
Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu ta Jihar Jigawa ta ƙaddamar da sabbin injinan samar da ruwan sha masu ƙarfin KB 250 da KB 150, tare da gyaran babban injin Mahadi Kature da ke haɗe da babbar tashar ruwan sha ta yankin, domin magance matsalar!-->…
Likita ɗaya na kula da marassa lafiya sama da 9,000 a Najeriya, likitoci sun ƙayyade iya awanni da…
Ƙungiyar Nigerian Association of Resident Doctors (NARD) ta bayyana takaici kan rashin daidaituwar adadin likitoci da marasa lafiya a Najeriya, inda kowane likita ɗaya ke kula da mutane 9,083 – lamarin da suka ce ya yi nisa da ƙa’idar!-->…
An zargi jam’iyyun siyasa da durƙusar da ci gaban Najeriya a shekaru 65 na ƴancinta
Manyan masu fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam a Najeriya, Femi Falana (SAN), da tsohon ɗan majalisar wakilai, Usman Bugaje, sun soki tsarin jam’iyyun siyasa a ƙasar a matsayin babban dalilin da ya hana ci gaban Najeriya shekaru 65 bayan samun!-->…
Ƙungiyar Malaman Kwalejojin Ilimi sun kai ziyarar ta’aziyya kan rasuwar haziƙin ɗalibi a Jigawa
Wata tawaga daga ƙungiyar Colleges of Education Academic Staff Union (COEASU) ta kai ziyarar ta’aziyya ga majalisar gudanarwa ta Kwalejin Ilimi ta Jihar Jigawa da ke Gumel, bisa rasuwar dalibi mafi ƙwarewa a fannin Mathematics/Physics na!-->…
Gwmnati ta rage kuɗin kujerar Hajji na 2026, akwai banbanci tsakanin yankunan Najeriya
Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta fitar da sabon farashin kujerar aikin Hajji na shekarar 2026, inda ta rage kuɗin da za a biya da kusan naira dubu 200 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
Rahoton da wakilinmu ya tattaro daga!-->!-->!-->…
Matatar Dangote ta dakatar da Sayar da man fetur da naira, za a iya samun canjin farashin litar mai…
Masana’antar Dangote Petroleum Refinery and Petrochemicals ta sanar da dakatar da sayar da man fetur da Naira daga ranar Lahadi, 28 ga Satumba, 2025.
Rahoton da wakilinmu ya tattaro ya nuna cewa, sanarwar ta fito ne daga Sashen Harkokin!-->!-->!-->…