Browsing Category
Ilimi
Labarai da bincike kan harkar ilimi da cigaba.
JAMB ta bayyana shigar wasu ɗinbin ɗalibai Jami’o’i a matsayin haramtacciya
Hukumar JAMB ta bayyana cewa ta gano ɗaukar ɗalibai 2,658 da aka yi ba bisa ƙa’ida ba a wasu jami’o’i, kwalejoji, da makarantun fasaha 17 a lokacin shekarar karatu ta 2024/2025.
Wannan na zuwa ne yayin da jami’o’in gwamnati suka kammala!-->!-->!-->…
Ƙungiyar Malaman Kwalejojin Ilimi sun kai ziyarar ta’aziyya kan rasuwar haziƙin ɗalibi a Jigawa
Wata tawaga daga ƙungiyar Colleges of Education Academic Staff Union (COEASU) ta kai ziyarar ta’aziyya ga majalisar gudanarwa ta Kwalejin Ilimi ta Jihar Jigawa da ke Gumel, bisa rasuwar dalibi mafi ƙwarewa a fannin Mathematics/Physics na!-->…
Atiku ya ɗauki nauyin karatun ɗalibai uku da suka lashe gasar Turanci a Ingila
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma jagoran adawa, Alhaji Atiku Abubakar, ya ɗauki nauyin karatun ƴan mata uku da suka lashe gasar TeenEagle Global Finals ta Turancin Ingilishi da aka gudanar a Ingila.
BBC Hausa ta tattaro a wata!-->!-->!-->…
Kano ce jiha mafi cin jarrabawar NECO a 2025, Gwamna Abba ya nuna farin cikinsa
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana farin cikinsa bayan da Jihar Kano ta zama jiha mafi samun nasara a jarrabawar NECO ta 2025 ga ɗaliban makarantu, inda ta zarce sauran jihohi a sakamakon ƙarshe.
A wani saƙo da ya wallafa!-->!-->!-->…
Gwamnati ta dawo da koyar da darasin Tarihi a kowanne fannin a makarantun Najeriya
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da dawo da darasin Tarihi a matsayin darasi na dole a makarantun firamare da sakandire.
Wannan mataki, a cewar ma’aikatar ilimi ta tarayya, na da nufin ƙarfafa kishin ƙasa, haɗa kan al’umma da kuma samar da!-->!-->!-->…
Jihar Jigawa ta karrama malamai ma su ƙwazo a fannin koyarwa da maƙudan kuɗaɗe
Gwamnatin Jihar Jigawa ta karrama wasu malamai na makarantun kimiyya da fasaha da suka yi fice a shekarar 2025.
An raba lambobin yabo da kyaututtuka na kuɗi domin nuna yabawa ga jajircewa da ƙwarewar da suka nuna.
Gwamna Umar Namadi!-->!-->!-->!-->!-->…
Gwamnan Jigawa ya tallafawa ɗaliban Maigatari da naira miliyan 2
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bayar da tallafin naira miliyan biyu ga wasu ɗalibai ƴan Maigatari da suka nuna bajinta a taron “Gwamnati da Jama’a” da aka gudanar a ƙarshen makon da ya gabata.
Wakilinmu ya tattaro cewa!-->!-->!-->…
OPay ya ƙaddamar da tallafin karatu na miliyoyin nairori da ɗaliban BUK, ɗalibai za su samu ₦300,000…
Kamfanin OPay Digital Services Limited ya ƙaddamar da wani shirin tallafin karatu na Naira miliyan 60 ga ɗaliban Jami’ar Bayero da ke Kano, a ranar Talata, 9 ga Satumba 2025.
Wakilinmu ya gano cewa an ƙulla wannan yarjejeniya ne ta!-->!-->!-->…
Hukumar NMCN ta soke dokar korar ɗaliban aikin jinya da ungozoma bayan kasa cin jarabawa sau uku
Hukumar Kula da Ilimin Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NMCN) ta sanar da soke doguwar dokar da ta daɗe tana tilasta wa ɗaliban koyon aikin jinya da suka kasa haye jarabawar ƙwararru har sau uku su bar makaranta.
Wakilinmu ya tattaro daga!-->!-->!-->…
SUBEB ta Jigawa ta buɗe ƙofar neman aikin zama Sakataren Ilimi na ƙaramar hukuma a jihar
Hukumar Ilimi Matakin Farko ta Jihar Jigawa (SUBEB) ta sanar da buɗe shafin neman aikin Sakataren Ilimi a fadin ƙananan hukumomi 27 na jihar.
Wakilinmu ya tattaro daga wata sanarwa da aka rarraba a madadin Shugaban Hukumar cewa, an buɗe!-->!-->!-->…