Browsing Category
Babban Labari
Muhimman manyan labarai na rana.
Ƴan Sanda sun cafke ɓarayi da ƴan fashi a Jigawa, sun gano babura da wayoyin hannu
Jami’an ƴan sanda a jihar Jigawa sun samu nasarar cafke mutane da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, ciki har da ƴan fashi, ɓarayin babura, da masu satar wayoyi, inda suka ƙwato babura uku, wayoyin hannu biyu da wuƙa daga hannun su.
!-->!-->…
Hukumar NMCN ta soke dokar korar ɗaliban aikin jinya da ungozoma bayan kasa cin jarabawa sau uku
Hukumar Kula da Ilimin Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NMCN) ta sanar da soke doguwar dokar da ta daɗe tana tilasta wa ɗaliban koyon aikin jinya da suka kasa haye jarabawar ƙwararru har sau uku su bar makaranta.
Wakilinmu ya tattaro daga!-->!-->!-->…
SUBEB ta Jigawa ta buɗe ƙofar neman aikin zama Sakataren Ilimi na ƙaramar hukuma a jihar
Hukumar Ilimi Matakin Farko ta Jihar Jigawa (SUBEB) ta sanar da buɗe shafin neman aikin Sakataren Ilimi a fadin ƙananan hukumomi 27 na jihar.
Wakilinmu ya tattaro daga wata sanarwa da aka rarraba a madadin Shugaban Hukumar cewa, an buɗe!-->!-->!-->…
Hasashen samun ruwan sama a sassan Najeriya na yau Talata daga NiMet, za a sami ambaliya a jihohi 2
Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa (NiMet) ta bayyana hasashen yanayi na ranar Talata, 9 ga Satumba, 2025, inda aka yi gargaɗin yiwuwar samun ruwan sama mai ƙarfi, hadari mai duhu, da yiwuwar samun ambaliya a wasu sassan Najeriya.
!-->!-->!-->…
A iya wata 1 a Najeriya, an kama masu laifi 1,950, an ceto 141, EFCC kuma ta ƙwato sama da naira…
Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa (NOA) ta bayyana cewa a watan Agustan 2025, ƴan sanda sun kama mutane 1,950 tare da ceto mutane 141 da a kai garkuwa da su, yayin da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci (EFCC) ta samu nasarar hukunce-hukunce 588!-->…
Muhimman abubuwa 10 da suka faru a rana mai kama ta yau, 8 ga Satumba
Kamar kowacce rana ta tarihi, a rana mai kama ta yau a shekarun da suka gabata, abubuwa da dama sun faru na tarihi, ga kaɗan daga cikinsu:
Boko Haram ta fasa gidan yari a Bauchi – 2010
A ranar 7 zuwa 8 ga Satumba 2010, ƴan ƙungiyar!-->!-->!-->!-->!-->…
Wasu jiga-jigan manyan Najeriya za su ƙaddamar da sabuwar tafiyar gyaran demokaraɗiyya a ranar…
Manyan masana da shugabannin fannoni daban-daban na Najeriya, ciki har da Farfesa Pat Utomi, tsohon Shugaban INEC Farfesa Attahiru Jega da tsohuwar Ministar Ilimi, Dr. Oby Ezekwesili, za su ƙaddamar da sabuwar tafiya domin neman gyaran!-->…
Mutane 63 ne suka mutu, ciki har da sojoji, a sabon harin da Boko Haram ta kai Jihar Borno
Fushi da alhini sun mamaye Bama a Jihar Borno bayan aƙalla mutane 63, ciki har da sojoji biyar, sun rasa rayukansu a sabon harin da Boko Haram ta kai a garin Darajamal, wanda aka dawo da mazauna cikinsa kwanan nan bayan gudun hijirar!-->…
NiMet ta yi hasashen samun ruwan sama da guguwar iska a yau Litinin a sassan Najeriya
Wakiliyarmu Maryam Ayuba ta tattaro daga Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMet) cewa hasashen yanayi na ranar Litinin, 8 ga Satumba, 2025, daga ƙarfe 12 na dare zuwa ƙarfe 11:59 daren Talata, ya nuna ana sa ran samun ruwan sama da!-->…
Za a sami rashin lafiyar wata mai tsanani “blood moon” a yau Lahadi a Najeriya da wasu ƙasashen…
Mutanen Najeriya da wasu ƙasashen Yammacin Afirka na shirin shaida wani gagarumin al’amari na sararin samaniya a ranar Lahadi, 7 ga Satumba, yayin da za a samu cikakken kusufin tun daga ƙarfe 8:00 na dare agogon Yammacin Afirka.
Rahoton!-->!-->!-->…