Browsing Category
Babban Labari
Muhimman manyan labarai na rana.
Tinubu ya ba da umarnin gaggawa ga ministoci na rage tsadar kayan abinci a Najeriya
Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya bai wa wani kwamiti na Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) umarnin gaggawa kan rage tsadar kayan abinci a kasuwannin ƙasar.
Wakilinmu ya tattaro daga jawabin Ƙaramin Ministan Harkokin Noma da Tsaron!-->!-->!-->…
Ƴan Sanda sun sake bankaɗo wata lalatar a Jigawa ta satar shanu da satar wayoyin lantarki, sun kama…
Rundunar ƴan sandan Jihar Jigawa ta ce ta samu nasarar daƙile satar shanu da kuma kama waɗanda suka lalata wayoyin wutar lantarki a wasu sassan jihar, tare da kama mutane da dama da ake zargi da hannu a cikin laifukan.
Wakilinmu ya!-->!-->!-->…
INEC ta amince da sabon shugabancin jam’iyyar ADC na ƙasa
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta tabbatar da sabon shugabancin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), lamarin da ya samu yabo daga ƴan jam’iyyar da kuma magoya bayan demokaraɗiyya a Najeriya.
Wakilinmu ya tattaro!-->!-->!-->…
OPay ya ƙaddamar da tallafin karatu na miliyoyin nairori da ɗaliban BUK, ɗalibai za su samu ₦300,000…
Kamfanin OPay Digital Services Limited ya ƙaddamar da wani shirin tallafin karatu na Naira miliyan 60 ga ɗaliban Jami’ar Bayero da ke Kano, a ranar Talata, 9 ga Satumba 2025.
Wakilinmu ya gano cewa an ƙulla wannan yarjejeniya ne ta!-->!-->!-->…
HASASHEN YANAYI: NiMet ta fitar da gargaɗi kan samun ruwan sama mai iska a yankunan Arewa da Kudu a…
Hukumar hasashen yanayi ta ƙasa (NiMet) ta bayyana hasashen yanayin yau Alhamis, 11 ga Satumba 2025, inda ta yi gargaɗi kan samun ruwan sama da ake sa ran zai biyo da iska mai ƙarfi a wasu sassan ƙasar.
Rahoton da wakiliyarmu ta tattaro!-->!-->!-->…
DA ƊUMI-ƊUMI: Najeriya ta shiga duhu, babban layin wutar lantarki na ƙasa, National Grid, ya katse
Sanarwar da hukumomin wutar lantarki suka fitar ta ce, babban layin wutar lantarki na ƙasa, National Grid ya samu katsewa a ranar Laraba, lamarin da ya haifar da katsewar wutar lantarki a sassa daban-daban na Najeriya.
A cikin wata!-->!-->!-->…
Kano ta haramta amfani da zarton inji marar izini a sare bishiyoyi, ta ɓullo da tsarin ba wa zartuna…
"Ba za mu ƙyale sare itace ba don na son rai kawai – ka sare ɗaya, sai ka dasa biyu ko uku,” in ji Hon. Dakta Dahiru Muhammad Hashim, kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na Jihar Kano, yayin bayyana sabuwar dokar haramta amfani da zarton!-->…
Rigimar dakatar da Natasha ta ƙara zafi, PDP da manyan lauyoyi sun caccaki Majalisar Dattawa kan ƙin…
Rigimar da ta shafi dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta sake ɗaukar sabon salo a jiya Talata, yayin da jam’iyyar PDP da wasu manyan lauyoyi (SANs) suka soki matakin Majalisar Dattawa na ƙin barin ta koma majalisa bayan cikar!-->…
Ƙungiyar Likitocin Asibitocin Gwamnati za ta yanke hukuncin ƙarshe kan tsunduma yajin aikin gamagari…
Ƙungiyar Likitocin Asibitocin Gwamnati ta Ƙasa (NARD) za ta gudanar da taron Majalisar Zartarwarta ta Ƙasa (NEC) a yau Laraba domin yanke shawara da ɗaukar mataki na gaba kan wa’adin kwanaki 10 da ta bai wa gwamnatin tarayya.
Ƙungiyar!-->!-->!-->…
Ofishin Birtaniya da UNICEF sun yaba wa Jigawa kan kula da muhalli da ciyar da ƙananan yara
Gwamnatin jihar Jigawa ta samu yabo daga Ofishin Birtaniya na Harkokin Ƙasashen Waje (FCDO) da Hukumar Kula da Yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) bisa yadda ta ke jagoranci wajen yaƙi da ƙarancin abinci da kuma gina makarantu da!-->…