Bayan an masa zanga-zanga, Gwamnan Kano ya amince a gaggauta gyaran Gadar Ƴanshana
“Za mu fara (aikin) nan da nan — Gadar Ƴanshana za ta dawo kamar yadda ya kamata,” in ji Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, yayin amincewa da gyaran Gadar Ƴanshana da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso, bayan da mazauna yankin suka gudanar da zanga-zangar lumana.
Wakilinmu ya gano cewa bayan zanga-zangar, Gwamnan ya ce a taron Majalissar Jihar na yau Laraba za a amince da a fara aikin gyaran nan take.
Gadar ta rushe ne kwanaki uku da suka gabata bayan mamakon ruwan sama, kuma tana haifar da matsalolin rayuwa ga al’ummar unguwar.
Har ila yau, Gwamnan ya umarci a kammala aikin wata makarantar sakandare da aka daɗe ana dakon gyaranta a unguwar, da kuma samar da sabuwar maƙabarta, inda ya umarci shugaban Ƙaramar Hukumar Kumbotson ya samar da fili domin wannan buri.