Annabi Muhammad (SAW): Gwarzontaka, Rahama, Da Nasarorin Da Ba A Taɓa Samun Irinsu Ba

19

A yau, 12 ga Rabi’ul Awwal, 1447, Musulmi a duk faɗin duniya na murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), fitaccen mutum ne da tarihin rayuwarsa ya ci gaba da shafar addinai, dokoki, ɗabi’u da al’adu a faɗin duniya.

An haife shi a Makkah a kusan shekara ta 570 Miladiyya, ya taso cikin halin riƙo da gaskiya da amana, ya zama mashahurin mai gaskiya (al-Amīn), sannan cikin shekaru 23 na kira zuwa ga Musulunci, ya haɗa ƙabilun Larabawa masu gaba da juna a wancan lokacin ƙarƙashin kalmar Allah ɗaya ne, a yi tafiya a kan tsarin adalci, da walwalar al’umma – juyin juya halin da masana tarihi ke cewa ba shi da tamka a tarihin ɗan Adam gaba ɗaya.

Daga farkon wahayi a shekara ta 610 a kogon Hira, zuwa Hijira zuwa Madina a shekara ta 622 – wadda ta zama sanadin samun kalandar Musulunci – Annabi Muhammad ya haɗa hangen nesa na harkokin imani da fasahar shugabanci.

A Madina, ya samar da yarjejeniyar haɗin kai wadda aka fi sani da Manhajar Madina, inda aka bai wa Musulmi, Yahudawa da sauran ƙabilu abokan hulɗa haƙƙoƙi da nauyi iri ɗaya, abin da masana ke kira da tsohuwar doka ta zaman tare cikin zaman lafiya.

A shekara ta 630, Annabi ya komo Makkah ba da fushi ba, amma da afuwa, ya tsarkake Kaʿabah daga gumaka, ya kuma yafewa maƙiyansa – abin da masana ke bayyanawa a matsayin ɗaya daga cikin manyan ayyukan rahama a lokacin nasara a tarihin bil’adama.

Shahararrun masana da masu tunani daga sassa daban-daban na duniya da na ilimi da fahimta sun tabbatar da girmansa.

Masanin falsafa daga Scotland, Thomas Carlyle, ya rubuta a cikin littafinsa On Heroes (1841): “Ƙarya… da aka tara a kan wannan mutum, kawai abin kunya ne a gare mu.”

Masanin tarihi Michael H. Hart, a cikin littafinsa mai tasiri The 100 (1978), ya sanya Annabi Muhammad a na farko, yana mai cewa, “Ya yi nasara ƙwarai da gaske a matakin addini da kuma na rayuwa.”

Marubucin Faransa, Alphonse de Lamartine, ya bayyana cewa: “Idan girman manufa, ƙarancin kayan aiki da kuma girman sakamako ne suke auna basira, wa zai kama da Muhammad?”

Masaniya Karen Armstrong ta ce: “Muhammad ya yi nasara sosai, ba kawai a siyasa ba har ma a harkar imani… Musulunci yana ƙara ƙarfi daga lokaci bayan lokaci.”

A yau, yayin da muke tunawa da zagayowar haihuwarsa, gadon da Annabi Muhammad ya bari abin koyi ne ga shugabanci na adalci, rahama, jarumta da hikima.

Saƙonsa ya haɗa zuƙata, ya gina cibiyoyi, ya inganta matsayin mata, ya hana kashe ƴaƴa mata, ya raya ilimi, ya yi kira da samar da daidaito a zamantakewa.

A wannan zamani na rashin tabbas, tarihin rayuwarsa ba kawai labarin addini ba ne; tunatarwa ce kan abin da shugabanci nagari zai iya cimmawa, wato samar da al’umma da aka gina bisa rahama, riƙo da gaskiya, da mutunta ɗan Adam – darajojin da duniya ke buƙata har yanzu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.