An zargi jam’iyyun siyasa da durƙusar da ci gaban Najeriya a shekaru 65 na ƴancinta

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Manyan masu fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam a Najeriya, Femi Falana (SAN), da tsohon ɗan majalisar wakilai, Usman Bugaje, sun soki tsarin jam’iyyun siyasa a ƙasar a matsayin babban dalilin da ya hana ci gaban Najeriya shekaru 65 bayan samun ƴancin kai.

Wakilinmu ya bayyana cewa, waɗannan furucai sun fito ne a yayin wani shiri na musamman da Channels Television ta gabatar domin bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ƴancin kai.

Falana ya bayyana cewa tsarin “winner-takes-all” na yanzu ya saɓawa salon siyasa na Jamhuriyya ta Biyu.

A cewarsa, “Ba za a iya mayar da dukkan ikon ƙasa ga jam’iyyar da ta ci zaɓe kawai ba. Dole ne a riƙa rabon iko da sauran ɓangarori. Rashin jam’iyyun da ke da tsarin ra’ayi da manufa shi ne tushen rashawa, rashin gaskiya da rashin ladabi da ake fama da su.”

Bugaje, a nasa ɓangaren, ya nuna cewa rashin ingantaccen tsarin zaɓen shugabanni na tasowa ne daga rashin manufa a jam’iyyun siyasa.

Ya ce jam’iyyun na yanzu “kamar jikin da babu rai ne, babu bambanci tsakaninsu, don haka ake yawo daga jam’iyya zuwa jam’iyya ba tare da wata matsala ba.”

Ya ƙara da cewa, “Na sha faɗa: Jam’iyyun siyasar da muke da su yanzu ba su da komai ko mutunci, babu jarumta, ba su dace da komai ba. Me ya bambanta PDP da APC a yau? Babu.”

👍 Ku bi shafinmu na Facebook

Don karanta labaran mu kai-tsaye a Facebook

Leave A Reply

Your email address will not be published.